LABARAN KARSHEN MAKO

Yau lahadi 8-9-2019

Cikin Labaran zakuji crea

Wasu daga cikin 'yan wasan Barcelona sun yi tayin yin amfani da kudadensu wajen sayen tsohon abokin taka ledarsu dan kasar Brazil mai shekara 27, Neymar daga PSG a lokacin bazara bisa yakinin da suke da shi cewa idan ba Neymar to zai yi wa kulob din wuya ya samu nasara a gasar Champions League. (Marca)
Cristiano Ronaldo lokacin da yake nuna goyan bayansa ga palasdinawa

Juventus zai fara tattaunawa da mai tsaron ragar Manchester United, David de Gea a watan Janairu, lokacin da kwantaraginsa da kulob din zai kare, in ji jaridar (Sunday Express)

Man United din dai na gab da kammala duk mai yiwuwa wajen nada tsohon mai tsaron ragarta dan asalin kasar Netherlands, Edwin van der Sar a matsayin darektan kwallo na kulob din, kamar yadda (Sunday Mirror) ta rawaito

Real Madrid za ta yi kokarin sayen dan wasan gaba dan faransa, Kylian Mbappe mai shekara 20 daga Paris St-Germain a bazara mai kamawa. (Sport - in Spanish

Manchester City za ta taya dan wasan Inter mIlan mai shekara 24, Milan Skriniar a watan Janairu, a kokarin Pep Guardiola na magance matsalar da suke da ita a bayansu. (Sunday Express)

Virgil van Dijk, mai shekara 28, ya amince da sabuwar kwantaragin shekara shida da
Liverpool. (Sunday Mirror)

Dan wasanJuventus na gaba, Juan Cuadrado, mai shekara 31 zai fara tattaunawa da kulob din domin sanin makomarsa bayan da kwantaraginsa za ta kare. (Goal

Dan wasan gaba dan asalin kasar Ingila mai shekara 20, Eddie Nketiah, na gab da koma wa Leeds United daga Arsenal
domin sama wa kansa kujera a kulob nan gaba, (Mail on Sunday)

ManajanSevilla, Julen Lopetegui na son sayen dan Nacho Fernandez, dan kasar Spaniya mai shekara 29 daga Real Madrid a lokacin bazara. (Marca)

Napoli na shirin tsawaita kwantaragin dan wasan kasar Spaniya na baya, Fabian Ruiz a kulob din. Idon kulob din Real Madrid dai na kan dan wasan mai shekara 23. (Football Italia)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post