Harin Saudi Arabia: Miƙa wuya ga maƙiya ba ya cikin ƙamus ɗinmu - Birgediya Salami
![]() |
Matatun man fetur din saudiya da aka lalata |
Kwamadan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na ƙasar Iran Birgediya Salami ya ƙara jaddada cewa, "Miƙa wuya ga abokan gaba ba ya cikin tsarinmu".
Kwamandan ya ƙara aikawa da wannan saƙon ne a cikin wannan makon a lokacin da ake tsakar cecekuce kan iftala'in rugujewar tattalin arziƙin Saudi Arabia a sakamokon harin mayaƙan Houthi Ansarullah na ƙasar Yamen da suka kai a babbar ma'aikatar man fetur din ƙasar Saudi Arabia a safiyar Asabar din da ta gabata.
B. Janar Salami ya taɗa isar da irin wannan tsatstsaurar saƙon ga maƙiya a ranar 8 ga watan Satumbar nan da muke ciki 2019, a yayin da yake gabatar da jawabi a gaban babban taron Tasu’a a birnin Janjan dake Arewa maso yammacin Iran.
Birgediya Salami a wancen lokacin ya ce, "Yunƙurin Ashura ya tabbatar da cewa, gwgawarmaya da tsayin daka da turjiya su ne miƙaƙƙun hanyoyi masu kaiwa ga sa’ada. Kuma a wannan lokacin, dukkanin duniya tana jinjinawa al’ummar Iran saboda yadda take ƙalubalantar
ƙasashe masu girman kai ".
"Bugu da ƙari, Birgediya Salami ya ce, miƙa kai ga maƙiya ba ya cikin
ƙamus dinmu, kuma manufarmu ita ce tsayin daka da samun ƙarfi". In ji shi.
Tags:
Labaran Duniya