KYAKKYAWAR MACE



Fahimtar mutane game da kyau ta bambanta, kamar yanda fahimtarsu a dandano ko kala ya bambanta! A yayinda a fahimtarka farar mace itace kyakykyawa, wani zaka samu Baqace jarumarsa, a yayinda kake son mace mai qiba, wani kuma siririyace zabinsa, ayayinda kake fifita doguwa, wani gajera tafi masa, duk sifar da tafi maka, to zaka samu wani baya sonta!

A duk sanda ka samu macenda kake gani duk duniya ba kamarta, baka ganin aibu ko muninta, wani baida abinda ya tsana kamarta!
Shin don bata da kyau ne? Ya akai ta maka kyau har ka zabeta, amma wani ya tsaneta yake ganin muninta? Shin to menene kyau?

A tunanina kyau qaryace kawai, tamkar kawalwalniya ne dake gizo a idon matafiyi maijin qishi! Haka kyau yake gizo a ido da qwaqwalwar masoyi, hakanan muni yake gizo da kawalwalniya a ido da qwaqwalwar maqiyi!

A lokuta da dama, duk sanda muka kamu da son mace, zamuga duk duniya babu mai kyawunta, ba abinda mukeso sama da ita, bamu ganin muni bare laifinta, amma da zarar mun rabu, sai muga ta koma mummuna abar kushewa, shin kyawun ya barta ne, kokuwa ta sauya kamanni ne, kokuwa Kyau tsuntsune dake sauka akan mutum ya tashi a sanda yaso?

A duk wannan tsawon kaikawon, MACE itace mai shan wahala akan kyau, akullum burinta ta gamsar da MAZA cewa ita kyakykyawace, dukda samun yardar mutane abune mai wahala mara yiwuwa, hakan ke kaisu ga shafe shafe (bleaching), feqe feqen haqora, aske gira, qarin gashi, qari/ciko a 

jikkunansu don cike wata gaba dakeda komada ko tawaya a tunaninsu da sauran salo don kama zukatan maza!
Yar-uwa, a sanda kika soma bleaching don ki zama fara, ya zakiyi da mazan da ke son Baqar mace? Kokuwa kinga duk farar mace aureta ake baqa ke kwantai?
Ya zakiyi in kika gama bleaching din kuma baki samu masoyi ba fa?


Idan kikaje aka feqe haqorinki don kiyi wushirya, to ya zakiyi da wadanda basuson mai wushirya, kokuma masuson wushiryar su gujeki don ba kalar taki suke so ba?
A sanda kikaje kina ta kankare kankare da aske aske da ciko, ya zakiyi da wadanda sukuma duk wadannan abubuwan basuyi musu ba, basu son masu su?
Kada ki mance nawane matayen dake da sifar dakikeson komawa kalar tasu suke gararanba a titi basu samu mazajen aure ba? Idan wannan sifar ko kyau ce ke sa aure, me yasa basuyi auren ba?
Nawane baqaqen mata da kike kallo munana suke dakin mazajensu sunyi aure, nawane matayenda zakiga kaman aje filin tashe dasu don tawaya da muni, amma sun samu mazajen aure, suna dakunansu? Nawane kin fisu kyau da kamun kai, gashi sunyi aure amma ke baki samu miji ba? 

A qarshe dai zakiga kawai kyau abune mai wahalar riska, kyau wata masiface dake wahal dake, duk iya abinda zakiyi bazaki taba gaggauto da abinda Allah ya jinkirta ba, bazaki iya jinkirta abinds Allah ya gaggauto dashi ba!
Yar-uwa ki sani Ke kyakykyawace a idon wani, koda kowa na ganinki mummuna, koda kowa ya gujeki, akwai wani na nan na neman daman samun ki! To akan me zaki damu da mai sukarki maimakon mai yabon ki? Akan me zaki damu da masu kusheki akan masu yabawa dake?  

Ki sani  WALLAHI KE KYAKYKYAWACE,


 gwaninkine kawai bai zo ba, lokacine baiyi ba!
      –Adam Abu-Umayrah

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post