*1--MAUDU'IN DA AKA BANI SHI NE AIBUN RIYA, DA YIN ABU DAN ALLAH.
Daga Dakin Karatu Na Shafin Ma'asumah Wanda Adamu Muhammad guda ya gabatar a dakin Karatun Wakilan Shafin Ma'asumah..
Domin Yan uwa musamman yan Media dama wadanda keyin Abu domin A yabesu.....
An samu Hadisi daga Imam Jafar (a.s) yace:- " Dukkan Riya shirka ce, domin duk wanda yayi aiki dan muta ne to sakamakon sa na ga mutane. Wanda yayi aiki dan Allah to sakamakon sa naga Allah. "
Riya Itace: bayyana aiki mai kyau ko siffa abar yebo ko kuma wata Akida ta gaskiya dan neman matsayi a gun muta ne. Wannan kuma yana da matakai daban daban
Na farko nada matakai bayu:
1A-- Bayyana Akidar gaskiya ko sanin Allah dan neman suna a tsakanin mutane cewa kai mai Addinine ko mai Ilimi, dan samun matsayi a zukatan mutane.
Kamar yace: Ni bana dogaro da kowa sai Allah. Ko kuma yana yebon kansa a hikimance.
B- Yari ka nisanta kansa daga Akidu na bata, yana tsarkake kansa, dan kawai ya burge mutane suna darajanta shi, daidai ne yana yine kai tsaye a maganar sa ko yana Ishara ne da dabara.
2- Na biyu shima yana da matakai biyu:
A1- Ya bayyana kyawawan dabi'u na daukaka.
B- Ko kuma ya barrantar da kansa daga duk abinda ke kishiyantar hakan.
3- Itace Riyar da aka sani a gurin Malamai magabata (R.A) shima yana da matakai biyu.
A- Yin aiki ko wata Ibadar da shari'a ta koyar ko kuma wani Abu wanda a hankalce yana da kyau dan burge mutane da samun matsayi a gurin su.
B- Ko yabar abinda aka haramta ko karhanta dan manufar da aka ambata asama.
2 Kasani Ita Riya a cikin Tussan Addini da Sanin Allah, tafi tsananin Azaba a kan dukkan nau'o'in Riya da mummunan sakamako, kuma tafi tsananin duhu daga dukkan nau'in Riya.
Mai wannan aiki in ya kasance dama asali niyar sa burge mutane to shi Munafikine kuma zai tabbata a Wuta Azabar sa itace mafi tsananin Azaba.
In kuma yana da niyar aikin dan Allah ne sai kuma ya gwama da riyar, to duk dai shi ba Munafiki bane ta amma Riyar sa zata na dushe hasken Imani daga Zuciyar sa, ya kuma shigar da duhun kafirci a zuciyar sa.
Shi wannan mutumin ya zama mushiriki a buye ( a zuciya ) domin sanin Allah da kuma Akidu masu kyau da suka dace ayisu dan Allah amma sai shi kuma ya gwama Allah da wanin sa, ya kuma sanya shaidan yana yin tasarrufi a zuciyar sa, sai ya zama ita wannan zuciya ta zam ba ta allah ba.
Saboda haka, ya kamata ace duk wani aikin da mutum zai yi, to, ya tsarkake ninya. Domin rashin tsarkake ninya yana bata ayyuka.
Kamar yadda yazo ne cikin wani hadisi daga Manzon Allah (S) yake fada game da masu yin ayyukansu don nunawa mutane (riya).
Gobe kiyama Allah zai cewa wadanda suke yin ayyukan su don wann say:-
" KU TAFI ZUWA GA WADANDA KUKE NUNA MUSU AYYUKAN KU A DUNIYA, KU DUBA KU GANI SHIN ZA KU SAMI SAKAMAKO A WAJENSU?"
Amsar a bayyane take, kowa yasan babu mai bada sakamakon ayyukan bayi sai Allah ta'ala.
Kenan duk wani abinda za kayi matukar ba za ka samu ladansa wajen Allah ba, to yinsa ba shi da amfani gare ka.
3--- To kuma irin wannan dabi'a matasayin ta a Muslunci yana da matikar muni domin tana kai me ita matsayin shirka kamar yadda hadisi ya tabbatar da haka:-: " Dukkan riya shirkace. "
Domin ya maida kyak-kyawar hanyar da za'abi a hadu da Allah lafiya, ya sauyata da mafi kaskanci, ( neman yardar mutane) ya canja hasken Imani dake zuciya da duhun munafirci da shirka.
Kuma ka maida shiyayar duniya da lahira ta zama nisantar Allah maimakon kusanta, yanzu kana jin ka shiryaw duhun da ba haske bayan sa.?
Tsananin da ba ranar ranar yayewar sa.?
Rashin lafiyar da ba a tsammanin warkewar ta. ?
Mutuwar da babu rayuwa mai dadi bayanta.?
Wutar da take kona zuciya da konewar da zuciya ta da taka ba zasu kubuta ba ( sai in sunyi aikin korai.)
Itace wutar da Allah ya bamu labarin ta a wata aya mai girma have:- " Wutar Allah mai huruwa, wadda take lashe zukata " Idan aka rasa tauhidi kuma shirka da kafirci suka maye gurbinsa to a wannan lokacin ko ceton masu cetoma baya riskar mai wannan matsayi, zai tabbata cikin Azaba Allah ya sauwake.
4---- Ya kai mai daraja ka kasance mai taka tsantsan, kayiwa kanka hisabi a ko wanne aiki, kayi magana da kanka ( ruhinka ) kana mai tura shi ( ruhin ) zuwa ga aikin alkhairi da al'amura madaukaka.
Shin meke sanya ka yin tambaya akan mas'alolin sallar dare ko kuma taraddudi akan zikirori. ?
Shin wai kana son ka fahimci hukunce--hukuncen sallar daren ne ?
ko kuma kana son ka koyar da itane ?
( ka koyar da sallar ta sigar tambaya )
In haka ne ( koyarwanne) Dan neman kusanci da Allah ne.?
Kodai kana son nunawa mutane kai mai sallar dare ne ?
Me yasa kake son bawa mutane labarin ayyukan ka na boye ?
Me yasa kake yin sadaka a boye kuma ka fito kana bada labari ?
Me yasa in kayi wani abu na alkhairi kake so sai mutane sun san kaine kayi ?
Me yasa baka son yin akin alkhairin da baza azan Maine nayi ba.?
Misali kamar in kana daya daga cikin member na wani Shafin sada zuminta wanda in anyi rubutu sunan shafinne me bayyana kuma zaifi isar da sakon harkannan, amma sai ka kasa yin rubutu anan, kuma kayi a profile dinka.
To in abin ni in bada shaworine sai ince yi a wancan group din yafi kayi a naka shafin domin mutane da yawa zasu amfana fiye da in a profilebdin kane kayi.
To idan ya zama hakan dan Allah ne kana sone su sani dan suyi koyi, bisa hujjar cewa :
" Wanda ya sunnanta sunna mai kyau yana da ladanta ( ladan aikin sa ) da ladan Wanda duk yayi koyi dashi har zuwa ranar tashin kiyam... "
To bayyana shi na dakyau, kuma ka godewa Allah akan akan ( dacewa ) da ruhi tsaftatacce da zuciya tsarkakankiya.
To amma dan ritsawa da kuskure a filin fafatawa da zuciya wajen kokarin dawo da ita hanya, da kuma kau cewa makircinta , kar ta rudeka ta karkatar maka aikin alkhairi ya koma riya, sai akiyaye
.3--- Domin kar ayyukan alkhairi da za'abi a hadu da Allah lafiya ka sauya su da akasin su.
Ya kai abokin magana ( MAI RIYA ) Yanzu ka gamsu shiriyayar duniya da lahira ta zama nisantar Allah maimakon kusant..
5--- *NUSARWA**
Akwai abinda ya kamata mulura dashi wanda yake tasiri wajen magance wannan ciwo na zuciya ( sato riya ) shi wannan abin luran ya dace da *HUJJOJI* daga Alkur'ani mai girma, Hadisan Manzon Allah ( s.a.w.w. ) da na Limaman shiriya ( Imamai ) a.s sannan kuma hankali zai gaskata shi.
Domin shi wani sakamakone dake nuna iko na Allah madaukaki akan dukkan halittu da shimfiduwar mulkin sa bisa ga dukkan samammu, domin zukatan Bayi gaba daya suna karkashin tasarrufin sane suna kuma karkashin ikon sa.
Ba wanda yake da ikon juya zukata indai bada Izinin Allah da horewar sa ba.
Kai harma su masu zukatan akan kinkan su basu da sakakken iko na yin tasarrufi ( sakakke ) saida izinin Allah, to kuma an samu isharori da bayyanannun sakonni wanda suke nuna hakan daga Alkur'ni da Maganganun Ma'asumai ( a.s )
Sabida haka ka sani Allah shine mamallakin zuciya kuma shi yake juya ta yadda yaso, kai mai rauni ne baka da ikon yin tasarrufi da zuciyar ka in bada izinin Allah ba, kai dukkan manufofin ka da burace-- sauran halittu gabaki daya suna yiwuwa ne da Izinin allah.
To riyar ka da son burgewr ka, in kana yine dan jawo zukatan mutane gare ka, da jawo hankalin su dan ka burge su, ko dan ka samu matsayi a gunsu, ko kuma dan su soka ( to kayi hasara ) domin ma mallakin zuciya yana juyata ne yadda ya so, zai iya yiwuwa ( kayi aikin da ya kamata ka burge ko a soka ) amma ka samu akasin abinda kake tsammani.
Kamar yadda hadisi ya tabbatar cewa:-
" Wanda duk yake son haduwa da Ubangijin sa ( lfy ) to yayi aiki mai kyau kuma kar ya gwama Ubangijin sa da kowa a Ibada." Akkur'ani
Sai Imam (a.s) yace: " Mutum zayyi wani aiki na lada amma bayyi dan neman sakamako a gun Allah ba, ya zama dan neman tsarkake kai ne a gun mutane, yana burin mutane su ji ( yana aiki mai kyau ) to shi wannan shine wanda yayi shirka da Allah. Ba wani bawa da zai nayin Kyak-kyawan aiki a boye face Allah ya bayyanar da kyak-kyawan aikin sa, ba
*Daga Shafin Ma'asumah Nigeria News Update a Karatun da mukeyi duk kullun ga Wakilinmu a dakin karatu Tare da Wakilinmu Adamu Muhammad.*
Akwai yi Domin Allah, yananan zuwa..