MAGANAR MATSALOLIN DA BABBAN ASIBITIN DAURA YAKE FUSKANTA DA MAKAMANTANSU, INA HON. NASIR YAHAYA, INA HON.FATUHU MOHAMMED, KUMA INA SANATA BABBA KAITA??
Babban aikin zababben wakili musamman na siyasa shine kare mutuncin al'ummar da suka zabeshi tare da nemamasu yan'cin su.Ta hanyar gwagwarmaya da kuma ruwan sanyi.
Wannan tasa aka samu matakai har guda ukku na zababbu Wanda suka hada da wakilin jaha, tarayya, da kuma sanata. Don haka baya halatta ga wakili na kwarai yaga ana Neman danne hakkin mutanen sa yayi shiru, idan kuma har yayi wani yunkuri na tare musu fada to yana da kyau ya fito fili ya bayyana tunda harkar siyasa akeyi bare ace anyi riya.
Dalilin yin wannan rubutu shine a yan kwanakin nan wasu abubuwa sun faru a game da babban asibitin Daura inda akayi zargin yunkurin dauke injin generato na asibitin, DUK DA DAI BINCIKENA YA TABBATAR MANI DA CEWA INJIN BAYA AIKI A LALACE YAKE SAI ANYIMASA GYARA, BA KAMAR YADDA MUKAYI ZATOBA TUN FARKO MUN DAUKA MAI AIKI NE ZA'A DAUKE.
Gabanin afkuwar daukar wannan inji yan hadakar kungiyoyi na Daura sun hana faruwar wannan yunkurin ta hanyar dakile masu daukar injin, saidai bayan afkuwar lamarin wasu maganganu sunyita fitowa akan dama an dauke Abu kaza, an dauki kaza, an kuma dauki Abu kaza. Wait duk a cikin asibitin.
Wannan tasa naga yadace inyi kira ga wakilanmu, sufa Sani wannan yunkurin da yan kungiyoyi sukayi aikin kune Ku wakilai domin shine abin da muka zabeku kuyi mana, matukar don mu kukeyi. Yakamata Ku bazama Ku nemo amsar yunkurin daukar wannan inji da kuma abaibadan da akayi zargin an dauka, KU GANO WANENE YAKESAWA AKE DAUKA, KUMA IDAN AN DAUKA INA AKE KAIWA?
Nayi maku wannan matashiyane domin Ku wanzar da zaman lafiya cikin al'umma kada Ku bari daidayakun mutane su rika daukar doka a hannunsu, domin KUTURU DAYAGA MAI KYASFI CEWA YAYI DAGA NAN MUKA WUCE.
Idan kuma bazaku iya kare mana tare da karbar mana hakkinmu ba to gaskiya Ku bada waje masu himma su maye gurbinku. Domin bazamu yarda da TALASURAN WAKILAI BA.
Daga karshe muna sauraren Ku cikin gaggawa Ku taramu a wani lokaci a wata rana a wani waje Ku fadamana abin da bincikenku ya gano, domin mu fita daga layin shaci fadi, na masu zama teburin mai shayi. Idan kuma kun gano yadda lamarin yake Ku hana sake yunkurin faruwarsa ko wani Abu mai Kama da haka.
Musa Ibrahim Daura
19-9-2019.
![]() |
Sarkin Daura umar farooq kenan da tawagarsa yayin wata ziyara a Babban Asibitin Daura. |