BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA GWAMNATIN NIGERIA



M.N.U 030

MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE

Zuwa ga gwamnatin Nigeria ta farar hula karkashin jagorancin general Muhammadu buhari dan Adamu barawon agwagwa da yan kanzaginsa musamman nasiru el-rufa'i dan mahaukaciyar kasuwa.
Duk da cewar nasan nasiha bata maku amma duk da haka zanyi amfani da wannan damar don ganin na sauke hakkin ku akaina. Shin wai ku bakwa tunanin akwai lahira? Ranar da ba mulki ba sarauta? Ba nasaba ba dukiya? Ba iyali ba duk wani gata da matsayi da kuke takama dashi? Shin wai ko kun manta da wuta da aljannah ne? Shin kun manta da Allah yana azaba ga bayin da suka fandarewa umarnin sa a doron kasa ba? Shin kun manta dukiya mai karewa ce kamar yadda rayuwa take karewa ba? Shin bakwa so Allah ya saka ku cikin aljannah madaukakiya? Idan kun kasance cikin bayi managar ta!
In tambayeku mana? Don Allah wane irin farin ciki kuke tsintar kanku aduk lokacin da kuka kebance da iyalanku ko yayayen ku? Me yasa bazaku tuna cewar ko wane magidanci haka yake ji ba? Ba zaka taba gane farin ciki ko bakin cikin da ya samu wani ba har sai ka dauki wannan abun ka dan gantashi da kanka.
Don Allah ku dauki abinda kukayima sayyid zakzaky (h) ku dangantashi da kanku! In ku aka yi ma ya zakuyi? Shin bazakuyi tunanin cewa duk abinda kukayi akwai wadanda sukayi kafin ku ba, kuma Allah bai basu nasara ba? Ku tuna abinda kakannin ku suka yima shehu usman dan fodiyo mana, amma ya zame masu tamkar kunama suka kasayin nasara akansa ba?
Imam khumaini (k.s) wane irin nau'in jarabawa ne bai gamu da ita ba? Ciki harda barin mahaifar sa zuwa gudun hijira, amma karshe shine ke da nasara,shin wannan bazai ishe maku aya ba?
Maulana sayyid zakzaky (h) shi daya ransa amma idon duk kan kafirai da mush'rikan bayin duniyar nan na kansa, saboda yana kira adawoma tafarkin Allah a ajiye constitution adauki alkur'ani shiyasa aka far masa da kisa da dauri shi da duk wani wanda zai taimaka masa!
Yaku shugabannin kasar nan ku sani cewa Allah yana aramaku rana ne kuna abinda kuke so, amma akwai ranar da zaku girbi ayyukan ku. Sannan ina maku albishir da cewa bazaku taba yin nasara akan sayyid zakzaky (h) ba kamar yadda wadan da suka gabace ku basuyi nasara ba.
Daga karshe mu almajiran sayyid zakzaky (h) muna kara tunasar daku cewa abinda kukayi mana bamu manta ba bakuma zamu manta ba sannan bamu yafe ba sai mun dau fansa kun gadarma iyalan ku kamar yadda zamu gadarma iyalan mu!  Sannan muna kara kira agareku da babbar murya da ku gaggauta sako mana jagoranmu ya dawo cikin mu idan kuma kunki to wallahi zamu biyo maku ta bayan gida ta inda tunanin ku bai baku zamuyi ba, domin mu da Allah muka kama ba makami ba.don haka mu zuba mu daku!!!! Jinai nan da kuka zubar mana ya ishe ku haka nan.
#Free zakzaky
#Free ummah zeenat
#Free sheikh turi
#Free Mahadi tukur almizan
#Free jibril usman sarki
#Free my another brothers and sisters
Sakina Ahmad
MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post