Basuyin Rubutu Mai kyau bare su cikasa Ka'idojin Rubutun Hausa.




Abbakar Ibraheem Kudan daga hagu a layin farko Wajen Seminar da Wakilan Shafin Ma'asumah suka gudanar a kano


Amincin Allah Ya Tabbata a gareku yan uwana, ma'abota karamci. 

Da sunan Ubangijin kowa da komi (Allah)  tsira da aminci su kara tabbata ga Manzon tsira da Iyalan gidansa tsarkaka, gami da managarta Sahabbansa(r).

Da fari ina neman uzuri ga yan uwana bisa zuwana a kurarren lokaci, wannan ya farune a bisa wani dalili. Kunsan mu masu Iyali ba'a rasa mu da uzururruka, Madam ce ta aikeni. (dariya). Ina fatan yan uwana zasu amshi uzurina.

Na'am, kamar yadda sanarwa ta gabata cewa wai nine zan gabatar da tunatarwa dangane da 'Mai ake nufi da rubutun Hausa, Ya kuma ake yin shi, haka dokoki da kuma ƙa'idojinshi'. Wannan shine nauyin da aka dora min zamu tattauna tare da karawa junanmu sani a tsakaninmu. Don dama dukkaninmu dalibai ne.

Da fari bari na kasa maudhu'in gida uku, kamar yadda yazo don mu samu sauƙi wajan fahimta.

Bari na fara da 'Mai ake nufi da rubutun Hausa' a wannan janibin dai babu bukatar tsawaita dogon bayani domin babu wanda baisan mai ake nufi da rubutun Hausa ba. 

Saidai abinda zamu kafa fahimta shine; Shi rubutun da yaren Hausa rubutune wanda bashi da bambamci da kowane rubutu, face wajan sarrafa haruffan wajan yinsa, don bambamtasa da sauran yaruka, amma dukkanin harufan da ake amfani dasu wajan rubutun Hausa basu da bambamci dana turanci mai tsayi, face dai wajan sarrafa haruffan.

Akwai wadansu abubuwa daya kamata yan uwa mu lura dasu a duk lokacin da muke rubutu, musamman ma rubutun da zamu sakesa a duniya. To lallai ya kamata muyi taka tsan-tsan wajan kiyaye wasu dokoki da ka'idoji don guje bata rawarmu da tsalle.

Bari mu dan ɗauki wasu daga cikin wasu alamomi da ake amfani dasu wajan kyautata rubutun Hausa, wanda muke kiransu da ƘA’IDOJIN RUBUTU’. 

Amma ba wai zanyi bayaninsu ne dalla-dalla ba, illa iyaka zan dan haskawa yan uwa wasu ababen lurane game dasu

ALAMAR AYA (•)  Wannan alamace da ake amfani da ita don bayyanawa mai karatu cewa an kawo wata gaba ta dakatawa da karatu, kenan daga lokacin da mai karatu yaga wannan alama zai fahimci cewa wannan gabace ta tsayawa. Duk rubutun da zaizo bayansa sabo ne wanda ba lalai ya zama cigana dana fari ba. Kuma wannan wajibine ga duk marubucin Hausa ya kiyaye yadda ake amfani da ita, don rashin sanyata ko sanyata a muhallin da ba nata ba, yakan bata ma'ana baki daya. 

Misali; Yau ina gayyatarka biki a gidanmu. Shin zaka zo kuwa?

Idan ku lura zaku ga na sanya wannan alama ta aya, a daidai inda na kai karshen rubutu na. Shi rubutu na biyu bai shafi na farko ba, wannan dalilin ya sanya na raba tsakaninsu da alamar Aya.

Kuskurena babban na rubutasa kamar haka 

Yau ina gayyatarka biki a gidanmu zaka zo kuwa?  ×

Haka ma alamar dakatawa, wato comma (,) ita wannan tana da bambamci da Aya, ana amfani da itane a lokacin da akaso dakatawa a rubutu domin hutu, amma bisa sharadin a tabbatar da jimlar da za'a dakata a kai ta bada ma'ana. Muna yawan samun matsaloli wajan amfani da wannan alamar, fiye da kowace alama a cikin alamomin ka'idojin rubutun Hausa.

Misali; Naje makaranta yau, amma Malamai basu yi mana karatu ba. 

Idan mu lura zamuga cewa, jimloli biyune a cikin wancan, kuma na rabasu ta hanyar amfani da alamar dakatawa, duk lokacin da mai karatu yazo karatu to zai samu sauki wajan fahimta, kuma zai karanta cikin jin dadi da sha'awa.

Zan takaita da wadannan alamomin guda biyu, domin suna sufi bamu matsala wajan amfani, kuma amfaninsu yafi yawa da muhimmanci a cikin rubutu. Sauran suna da saukin fahimta wajan amfani. Sakamakon yanayi na lokaci ba zamu samu damar tabo kowanne daya bayan daya ba.

Sai kuma wani babban kuskure dana lura yayi tasiri sosai a cikin rubutun mu, shine, amfani da abbreviation wajan rubutu. Wannan babban kuskure ne sosan gaske, don bashi da muhalli Sam a cikin rubutu koma wane irine ne, ba wai sai Hausa kadai ba.

Na'am; mun maishesa yaren chatting, don saukakawa kawukanmu wajan tsawaita rubutu. Babu laifi idan ya zamana muna amfani da wannan ne wajan chatting kawai, amma sam bai kamata aka amfani dasu a cikin sauran rubutun da za'a yada a duniya ba.

Abin takaici da bakin ciki, a cikin satinnan nake ganin wani rubutu ana yadawa, amma sai ya zamana a Headline din rubutun anyi amfani da abbreviation, kuma da babban baki baro-baro kowa yana gani. Wai kuma a haka dan Media ne.

Wai anyi amfani da kalmar LFY a maimakon LAFIYA. Kuma babu wanda ya gani ya iya gyarawa, a haka ayita copy ana sharing din rubutun. Iya wayewa a nan? Mai al'umma zata daukemu, mu da muke ikirarin mun samu cikakkiyar wayewa daga wajan Jagoranmu. Alhali kullum Sayyid kokari yake wajan ganar da mu don gujewa irin wadannan kurakuran.

Na'am, akan samu kuskure wajan rubutu, musamman idan ana sauri a lokacin rubutun, wannan dalilin ne ma ya sanya aka kwadaitar da marubuta wajan kara bibiyar rubutu kamar sau biyu a duk lokacin da mutum yayi rubutu kafin ya sakesa, domin ba'a rasa kuskure a ciki ko kadan ne.
Yafi muhimmanci kayi rubutu mara tsayi cikin kyakyawar Hanya, akan kayisa da tsayi amma ba tare da kyautatasa ba. 

Lallai ya kamata yan uwa mu kiyaye wannan, musamman a lokacin da muke rubutun da samu sakesa ga duniya, koda za'a bata lokaci yafi muhimmanci ayisa da kyautatawa fiye da ace anyi ba tare da kyautatawa ba. Wannan dai shine

Akwai janibobi da daman gaske da ban tabo su ba, sakamakon yanayin lokaci, don na lura lokacin da aka diba min har ya wuce. 

Bisa wannan ya sanya dole  zan takaita a nan, don kiyaye lokaci da kuma tsari. 

Ina fatan yan uwa ayi min uzuri da afuwa bisa kwamacalar da akaji daga gareni, wannan ya farune sakamakon gazawata, dama na fada tun farko karawa juna sani zamuyi ba wai zan sanar da abinda ba'a sani bane.

Amma kafin muje ga tambayoyi, bari ba ba yan uwa wata tsaraba dana tsamo mana daga Taskar ma'abota abin. 

Yana da kyau Kowane dan uwa ya karanta da kyau, ya fahimta tare da amfani dashi wajan rubutunsa.

My Comment;

A ƙa'idar rubuta labari komai gajartarsa a kan so a fitar da abin da suke kira 5Ws & H.

Wato:
1- What = Me labarin ya kunsa/a kan meye?
2- When: Yaushe abin ya auku/Rana da lokaci?
3- Where: A ina abin ya auku?
4- Why: Saboda me/A kan me aka yi abin ko ake yinsa?
5- Who: Akan wa, ko a kan su wa ake labarin?

Sai kuma;

6- How?: Bayani gamsasshe na yadda abin ya faru daki-daki, dalla-dalla.

Wadannan kamar wasu rukunai ne na ingantaccen labari ta yadda duk labarin da bai kunshe su duka ba, to ana iya cewa ya gaza. Ba za a kira shi "News" ba.

Akwai bukatar dukkan yan Media dinmu da masu bamu labarai, ya zama suna kiyaye irin wadannan wajen kowane labarin da za su bada.

Misali:

*JAMI'AN TSARO SUN KAWO HARI A MARKAZ DIN NIJERIYA*

*Daga Wane Dan Wane.*

*Da misalin karfe 3:40 na yammacin yau Litini, 1 ga watan Maris, 2013 ne gamayyar jami'an tsaro suka kawo hari Markaz din yan uwa musulmi almajiran Shaikh Ibraheem da ke garin Nijeriya a jihar Arewa.*

Kaga a nan an fitar da WHAT? Lamarin meye? An kawo hari ne.

An fitar da WHERE? A ina abin ya auku? A garin Nijeriya jihar Arewa.

An fitar da WHEN? Yaushe abin ya faru? Da karfe 3:30 na ranar Litini, 1/3/2013.

An samu WHO ma. Wato mutanen da labarin ya shafa, yan uwa ne da jami'an tsaro.

Sai kawai a cigaba da labari a kasa, ko da kuwa Paragraph biyu ne, a ciki ai bayanin HOW; Yadda harin ya auku, da WHY; Dalilin aukuwarsa da kuma fadada bayanin WHO: Wato, mutanen da abin ya shafa in misali an samu Shahidai ko masu rauni da sauransu.

Amma sai ya zama yanzu kawai za ka ga rubutu ne layi uku. Kawai sai a ce *Yanzu-yanzun nan Yan sanda sun kawo hari a Fudiyyar garin Arewa.*  Sai wannan abin yai wata yana yawo kullum duk wanda ya gani sai ya dauka a lokacin ne abin ya faru.

Yana da kyau ya zama a kowane gari wadanda ake kira 'yan Media su rika shirya tarurrukan wayar da kan junansu, kuma su gayyaci wadanda suke bangaren Media na daga yan jarida da ke kusa da su suna koyar da su tare da tunatar da su yadda ayyukan suke. Allah Ya tausaya mana.
_____________

Malan inada tamyaba!!

Me wannan alamar take nufi kuma a ina ake amfani da wannan alamar  wato waqafi me ruwa (;)?

AMSA:-
Alamar waƙafi mai ruwa (;) alamace da ake amfani da ita a dai dai lokacin da za'a bayar da labarin da wani yace. 

Misali: Na taba jin Sayyid Zakzaky yace; “Hadafin Mu Shine Neman Yardar Allah”.  

Idan ka lura zakaga wannan alamar ta wakafi mai ruwa na kawota a dai-dai inda na rubuta Sayyid Zakzaky yace;....... 

A Gaskiya anfi amfani da ita wa irin wannan muhallin. Dukda akwai wasu guraren da ake amfani da ita, amma Gaskiya mafi yawanci anfi amfani da ita a irin wancan muhallin. 

Ana iya bincikawa littafan koyon ƙa'idojin rubutun Hausa da kuma Malaman Hausa don ƙarin bayani.



Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta'ala Wa Baraka Tu Hu. 

Wassallahu Ala Sayyidna Muhammadin Wa Ahlihil Adhar.

Wannan Shine Jawabin Abubakar Ibraheem Kudan Da yayi A dakin Taron Wakilan Shafin Ma'asumah a ranar lahadi 22-2019


Sai ta'alikin Comred nazeer Sa'idu Gusau gashi kamar haka:-

Comred nazeer:- Assalamu Alaikum, yan'uwa inaso idan anban dama,nadanyi ta'aliqi awannan jawabi na malan Abubakar Ibrahim kudan.

Kuma insha Allah zanyi bayanai akan wasu ababe da bai tabo ba.

Duk da lokacin da muke dashi takai tacce ne.
Idan na kammala rubutun zan sake shi awannan group din komai dare naha Allah.

Aikin muka fito kuma shi zamuyi dayardar Allah.

Assalamu Alaikum.

Bisa ga jawaban da babban bakommu yayi akan alamomin rubutu,nigga yadace nadanyi ta aliki acikin jawaban shi.

Babu shakka wannan mau'du in yanada fadi sosai.
Amma nima zan danyi qarin haske akan jawabansa,musamman idan nalura  lokacin da akabawa wannan malamin yayi qaranci yayi bayani akan wadamnan alamomi.

Aya, tana da nau’uka uku:
Babbar aya (.): Alama ce ta cikar Jimla da kuma bayar da damar tsayawa cik, ko kuma ƙarewar zance. Dokar rubutun Hausa a kanta ita ce cewa, dukkan harafin da zai biyo bayanta dole ya zama babban baƙi. Misali:
Isa ya ci tuwo.
Ɗanbarno ya zo da safe. Shi ya bar wannan hular  a nan.

Ayar tambaya (?): Alama ce da ke nuna cewa, dukkan jimlar da ta ƙare da wannan alama to tambaya ce. Misali:
Mene ne a ciki?
Ka shiga Rumbun Ilimi kuwa a yau?

Ayar motsin rai (!): Ana saka ta a bayan kalmar da ke nuna sosuwar rai, wacce ka iya zama ta farin ciki, baƙin ciki, razani, da sauransu. Misali:
Ahayye! Allah ya kawo mu.
Hahaha! Allah sarkin daɗi.
Wayyo! Ku kawo mani agaji.

Tagwan Ayoyi ): Tana da hukunce-hukunce kamar haka:
Cikakkiyar dakatawa.
Kawo maganar wani. Misali, Musa ya ce: “Ku sayo min gyaɗa idan za ku dawo”.

Jerin sunayen abubuwa.

 Misali, Ado yana sayar da kayayyaki irinsu:

 Littafi, alƙalami, jikka da sauransu.

Waƙafi (,): Alama ce ta dakatawa ta ɗan ƙaramin lokacin da bai wuce mai karatu ya shaƙi nunfashi ba. Ana ɗiga waƙafi a gurare kamar haka:
Gaɓar magana.
Gaɓar jimla.
Guraren da ake rarraba sunaye a cikin jere. Kamar ka ce Ado, Idi, Musa da Binta ɗalibai ne masu hankali. Idan aka lura a nan, waƙafi ne ya bambanta mana sunan Ado da na Idi. Dokar rubutu ta ce dukkan harafin da zai biyo bayan waƙafi dole ya zama ƙaramin baƙi.

Waƙafi mai ruwa (;): Alama ce ta gajeruwar dakatawa. Ana ɗiga ta a tsakanin jimloli biyu masu kama da juna waɗanda kuma kalma ta biyun ke zama cikwaton ta ɗaya. 
Misali: 
Babu wanda zai yi wannan aikin sai yara; domin su ne basu da hankali. Sannan kuma ƙaramin baƙi ne yake biyo bayanta.

Zarce (…): Ayoyi ne guda uku. Alama ce da ke nuna rashin ƙarewar zance. Suna iya zuwa a farko, tsakiya ko ƙarshen rubutu. Sannan kuma babu wata dokar rubutu da ta ce ga matsayin harafin da zai biyo bayanta. Kenan babba ko ƙaramin baƙi kowane na iya biyo bayanta. Ta zama abin da ake cewa, cinsa banza, barinsa banza kenan. Idan har mutum baya shiga shafin Rumbun Ilimi akai-akai, lallai…

Baka biyu (): Alama ce da ake amfani da ita a gurare kamar haka”
Ƙunshe ƙarin bayani game da rubutun da ya gabace ta a ciki.
 Misali:
Rumbun Ilimi (softuwayar kwamfuta cikin Harshen Hausa zalla), yana ɗauke da darrusa masu muhimmanci.
Haka nan kuma ana amfani da baka biyu wajen rubuta haƙiƙanin lambobin da aka rubuta adadinsu a cikin zance. Misali, jiya sun samu kuɗi har Naira dubu shida (N6000).
Wajen kafa hujjar wanda ya faɗi magana a cikin zance. Misali, Hausa tana da kalmomi masu gaɓa ɗaiɗai da yawan gaske (Yahaya, Zariya da ‘Yar’aduwa 2007).


Alamar zancen wani (“”): Alama ce da ake ƙunshe gundarin maganar da aka hakaito daga wani mutum a cikin zance. Misali, shi fa dama sai da ya ce: “Kowane ɗalibi ya kawo min nasa aikin da kansa”. Dokar rubutun Hausa ta wajabta fara rubuta harafin farko na abin da aka ƙunshe a ciki ya zamo babban baƙi.

Karan dori (-): Alama ce da ke ƙulle tsakanin kalmomi biyu su yi aikin kalma ɗaya. Ana ɗiga wannan alama a gurare kamar haka:
Gauraya ko haɗe kalmomi mabambanta. Misali:
 Bigi-bagiro, gam-da-katar da sauransu.
Ana amfani da ita wajen maimaita kalmomi iri ɗaya. Misali: daban-daban, akai-akai da sauransu.

Kara jirge (/): Alama ce da ake amfani da ta wajen bayar da zaɓin abu guda daga cikin jeri. Tana aiki ne a matsayin ko. Misali: Zauwa ga Alhaji/Hajiya, Ka/ki, kai/ku da sauransu.
Babu wata doka da ta yanke hukuncin matsayin harafin da zai biyo bayanta. Yana iya zama babba ko ƙarami.


 Alhamza (‘): Ana ɗiga wannan alama a tsakanin harrufa a cikin kalma ɗaya domin samar da cikakkiyar ma’ana. Dokar da za a kiyaye ita ce, cewa, ba a ɗiga ta a tsakanin tagwayen baƙaƙe (gw, sh, ky da sauransu). Misalanta sun haɗa da:
Mariya ‘yar’uwar Kande ce.
Anya kuwa wannan maganar da yake faɗa tana da ma’ana?
A taƙaice waɗannan su ne alamomin rubutun da za mu iya kawowa a wannan darasin. Idan mai karatu ya bisu daki-daki tare da kaifafa tunani, zai fahimci cewa suna taimakawa matuƙa wajen sauƙaƙa wa mai karatu karanta rubutu da fahimtarsa.


Insha Allah yan'uwa.
Ina fatar za ayi nazari akan wannan rubutu nawa .

#Comrade Naziru saidu sabty Gusau.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post