ZUWA GA AMINAN JUNA
Yaku aminan juna kusani cewa:-
Abokantaka ko kuma kawance tsakanin mutane ana yinsane da Wanda aka aminta da dabi'unsa da halayyarsa dama irin tarbiyyarsa, abonkataka tana da matukar muhimmanci tsakanin Al'umma don haka kasan dawa zakayi aboki ko kawance, abokin kwarai kamar mai saida turare ne ko ya sammaka ka shafa ko ya wuce kaji kamshi ko ka saya da kudinka don ka shafa kaji kamshi mai dadi ko don aji kamshi mai dadi daga jikinka,
shi kuwa mummunan aboki kamar mai hura wutar makera ne in ka zauna dashi kodai ya kona maka tufafi da tartsatsin wuta ko kasha qauri marar dadi, don haka nemi abokin kirki wanda zaku taimaki juna akan alheri kuyi alfahari da juna anan duniya da kuma lahira sannan ya rufa maka asiri ka rufa masa, in ya hango alheri ya nufoka ya taimaka don ganin ya iso gareka, in kuma ya hango sharri yayi kokarin kareka daga gareshi, aboki yana iya samun damar ceton aboki har a lahira, dan uwa ko yar uwa kusan dawa ya kamata kuyi abokantaka.
Allah ka azurtamu da abokai na kwarai.
–Abdul'Azeez Ibrahim Bauchi
Tags:
Muhimman zantuka