
KADUNA CAPITAL SCHOOL (KCS) A TAKAICE
Makaranta ce ta gwamnati wanda manufarta shine koyar da
'ya'yan talakawa.
Tun 1957 da aka bude ta, take koyar da 'ya'yan talakawa dana
masu kudi, a tare da haka kuma akwai Makarantu irinsu: Sardauna Memorial College (S.M.C), Kaduna Teachers College (K.T.C) da dai sauransu.
Duka Makarantun sun taka muhimmiyar rawa wajen bada karatu ga 'ya'yan talakawa da masu kudi.
Tafiya na tafiya har zuwa 1999 inda Makarantar Capital School
tayima sauran zarra kasancewar tana samun tallafi daga
gwamnati da kuma kwarin gwiwa wajen 'yan siyasa da masu
kudi.
Hakan kuwa baida nasaba da kasancewar Makarantar ta koma
ta masu kudi da 'yan siyasa.
Daga 1999 zuwa 2010 ba a daukan dan talaka a wannan
Makarantar, dole sai in uban mutum wani ne a siyasa ko kuma
wani dan siyasa yakai mutum Makarantar, amma haka kawai
baza a dauki dan talaka ba.
Nan el-rufa'i ne rike da dansa lokacin da ya kai shi Makarantar
Wannan fa itace Makarantar da EL-RUFA'I yakai dansa aketa
ihun yakai dansa Makarantar gwamnati, bayan kuma
Makarantar tafi karfin talaka.
Don haka EL-RUFA'I bazai burgemu ba sai yakai yaron sa L. G.E.A Unguwar Sarki, a nan ne zamu ce yayi kokari.
Muneer Yusuf Assalafy
23/09/2019
Tags:
Labaran Duniya