Da safiyar yau laraba 11/9/2019, da misalin karfe 8:30am,
a ka gudanar da Jana'izar Shahidai Biyu Shaheed Ibraheem
Abdullahi, da Shaheed Mustafa Nasiru Zikiri kaduna.
Idan mai karatu bai manta ba, su dai wadan nan
Shaheedai sun yi shahada ne sakamakon harin ta'addancin da
jami'an tsaron yan sandan Najeria suka kawo, a kan Masu
muzaharar Ashura, a jiya talata 10-9-2019 a junction din bakin
ruwa dake kan titin bypass daura da Hayin Rigasa a garin kaduna.
Anyi musu sallah ne a nan cikin Hayi daga bisani sai a ka kai
su makwan cin su, inda a ka bizne su anan. aka gabatar a
addu'o'i da dan jawabai, a kan masu afkar da shahada, da
tunatarwa a kan halin da jagora ya ke ciki da kuma yadda muka
samu kan mu, da nauyin da ya karu a kan mu game da iyalan
Shuhada, sannan akayi addu'a a ka watse.
Muna fatan Allah ya amshi Shahadar su tare da duk Shahidan mu ya kuma Kwato mana jagoran mu daga hannun azzalumai.
#Ashura1441
Tags:
Munasabobi

