-MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATE
A ranar talata goma ga watan satunba shekara ta dubu biyu da sha tara (10/09/2019) dai-dai da goma sha daya ga watan muharram shekarar dubu daya da dari hudu da arba'in da daya b.h, 'yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzakiy dake fadin kasar Nigeria suka suke bayyana a cibiyoyin jihohin kasar domin gudanar da muzaharar Ashura kamar yadda suka saba a duk farko-farkon shekarar musulumci, a tsawon shekaru masu yawan gaske.
Duk da dai a wasu lokutan musamman shekarun baya-bayan nan hukumomin jihohi da gwamnatin tarayyar kasar ta Nigeria sukan afka musu da kisa, kamu, azabtarwa da kuma sauran nau'uka na cutatarwa.
A ranar talatar ne bayan fitowar da sukayi 'yan uwa musulmin a birnin Kaduna jami'an tsaron kasar suka bude musu wuta babu kakkautawa babu saurarawa ba yaro ba babba, kuma sunzo wa muzaharar ne ta gaba da baya, jami'an sun bude musu wutane a lokacin da muzaharar take karasowa bakin ruwa.
Fara harbinsu ke da wuya Allah ya sanyawa 'yan uwan nutsuwa a zukatansu, ma'aikatan dake janibin gaba a muzaharar suka tunkare su aka fara dauki-ba- dadi, duk da cewa su 'yan uwan basu dauke da makami ko guda amman hakanan suka tsayu suka dinga kabbarbari suna neman dauki daga Allah.
Wakilinmu ya tabbatar mana da cewa 'yan uwa musulmin sun samu nasarar kora jami'an tsaron tun a farko, daga bisani wadanda suka zowa muzaharar ta gaba suka sake juyowa suka cigaba da yin harbin ba kakkautawa a kan wadannan mazajen.
Yayin zantawar wakilinmu da wasu mutum biyu daga cikin wadanda suka samu raunuka dayan cikinsu yace lallai jami'in da ya harbe shi a kafa yayi tamin dinsa ne domi yakai mintoci yana tamin dinshi, a lokacin da yake kwance yana tafiyar qaguwa (chronic) mikewar da zaiyi ya canza guri kawai sai ji yayi ya fasa mai cinya da harsashi, sanadin harbin da yayi masa kuma harsashin ya balla masa kashin cinya, karshe aka daukoshi aka fitar dashi daga gurin.
Niko banma san lokacin da suka yi min harbin farko ba domin 'yan uwa sunata cemin jini a hannunka banma san cewa dani suke ba, zan daga hannu kenan sai naji hannun yaki daguwa ashe har sun harbe ni ne, kawai sai na sake jin harbi na biyu wanda shine ya ballamin kashin hannu, dukka harbin a hannu guda. nima 'yan uwa suka zo suka dauke ni a gurin, cewar dayan da aka harba a hannu.
Akwai zaratan samarin da suka dinga shaukin karasowa gurin da ake waqi'ar domin ayi mu'araka dasu amman dake sunayin aiki ne a sauran bagarorin muzaharar babu yadda zasuyi dole suka hakura, akwai wadanda sukayi kuka akan cewa basa gurin kuma basu da daman karasawa gurin mu'arakan.
Daya daga cikin 'yan media forum na da'irar ta kaduna kuma wakilin Kaduna press yana daga cikin wanda harshi ya sama, sedai shi harsashin ya gogeshi ne a karkashin habarsa.
Duk da hakan bai hana zaratan matasa tsayuwa kyam ba wajan ganin sun baiwa jami'an tsaron wahalar gaske.
Zaratan samarin saida suka tabbatar sun kora jami'an tsaron nan sunyiwo cikin hayin rigasa da mungun gudun tsiya sannan suka dawo kan titin express way sukayi addu'a suka watse.
***
-Jabeer Bin Said Al'ansariy.
#RanarAshura1441.-11092019.
-12011441.
Tags:
Munasabobi
