*A Kaduna, 'yan sanda sun kashe mutum uku. Sun raunata da
dama, sun kama da dama. Çikin wadanda aka shahadantar
sun hada da; Shehu Mustapha, Abubakar Suleman.
*A Gwambe, da kuma yankin Misau-Giade A Azare ta jihar
Bauchi, Katsina, da Illelan Jihar Sakkwato, an harba tiya gas
da harsashi mai rai an kuma raunata mutum biyu a Gwambe,
sannan an shahadantar da mutum guda mai suna Sirajo
Muhammad Inuwa. A Illelan ma an raunata mutane da dama
tare da shahadantar da mutum guda mai suna Abubakar Jibo
Mai Magani.
*A Shinkafi, Tsafe, Mashi, Talatan Mafara, Kano, Abuja, Dabai,
Kauran Namoda, Jibiya, Daura, Potiskum, Minna na jihar Neja,
Birnin Kebbi, Kudan ta jihar Kaduna, Ramin Kura, Malam
Madori da Jahun a Jigawa, Damaturu, Gusau,Jos an kammala
lami-lafiya.
*A Zariya an kammala muzaharar lafiya, amma bayanai sun tabbatar da cewa sun kama wadansu daga cikin masu
muzaharar dake kan hanyar komawa gidajensu wadanda ba a
tantance ko mutum nawa bane.
*A Garin Goronyo dake Jihar Sakkwato, jami'an 'yan sanda sun
afkama masu muzaharar inda suka shahadantar da mutum
guda. Tare da jikkata wadansu.
*Har zuwa misalin karfe 9:56 na safiyar yau Talata, Jami'an
tsaro sun afka ma masu muzaharar Ashura a garin Bauchi.
Inda suka raunata mutane da dama tare sa shahadantar da
mutum guda mai suna Huzaifa.
*Sannan a garin Katsina, majiyarmu ta tabbatar mana da cewa;
Jami'an tsaron sun kai hari Markazin 'yan'uwa dake Katsina.
Inda suka harba Tiya gas da harsasai masu rai. Sun yi 6arin
wuta sosai. Kuma sun jikkata mutane da dama a muhallin. Sun
yi hakan ne bayan duk an gudanar da muzaharori a inda aka
tsara a Katsinan, duk da kame da musgunawa da suka rika yi.
Amma an yi muzaharori a wurare da dama a Katsinar.
*A Dutsin-Ma, 'Yan sanda sun kama 'yan'uwa da dama bayan
an kammala muzaharar, kuma sun raunata da dama a yayin da
suka kai hari tare da harba tiya gas. A Kankiya ma sun harba
tiya gas. Haka labarin yake a Malumfashi dake Katsina, inda
suka je har makarantar Fudiyya suka antaya wa al'umma Tiya
gas.
* A Yola ma ta jihar Adamawa, bayan an kammala muzaharar
lafiya, sun je wurin da aka rufe muzaharar suka yi mazurai. Har
suka je kusa da Fudiyyr garin.
*A Kontagoran jihar Neja, an jibge 'yan sanda inda za a tada
muzaharar, sai dai an samu nasarar yi duk da barazanar 'yan
sandan, amma sun yi yunkurin kama Wakilin 'yan'uwa na garin,
sai dai ba su yi nasara ba.
*Ina kan karkare rubutun nan, aka tabbatar min da cewa;
jami'an tsaro sun je gidan wakilin 'yan'uwa na Gwambe wato
Malam Abbare suka zagaye gidansa.
#RanarAshura1441
Tags:
MUNASABAR ASHURA
