_MUTANE SUKA JA MA KANSU QUNCIN ARZIKI
[FILIN_JAGORAN_GASKIYA_

_MUTANE SUKA JA MA KANSU QUNCIN ARZIKI


_Inji Jagoran Gaskiya [Sayyid Zakzaky]

_Abin da nake qoqarin in nuna a nan shi ne halin da muka riga muka shiga ayyuka ne na hannuwanmu. Kuma a nan babban laifin da ya janyo wannan bai wuce kangare wa Allah Ta’ala da aka yi ba.
Domin ta yiwu mutum ya ce, to yaya mu za mu sha wahala saboda fandara daga bin tafarkin Allah, su ko qasashen kafirai suna jin dadi? Sai mu ce, ai su (kafirai) ba su yi ma Allah karya ba; su ba su ce suna son Aljanna ba ballantana ma su sa rai da ita. Ba su kuma yi wa Allah qaryan Musulunci ba.
Kafirai suke, sun kafirce wa Allah kuma duniyar ta yi masu. Aljannarsu suke ci. Tsakanin su da wuta mutuwa. Saboda haka ko an sakar masu (duniyar), wannan ya yi daidai.
Kamar yadda aka ce duk lokacin da Allah Ta’ala ya aiko Manzo yakan takura mutane,
har idan sun wa'aztu shi kenan; idan kuma ba su wa'aztu ba akan yi masu ‘Istidraji’ har ranar kamun qarshe. To muna iya cewa,su qasashen kafirai an yi masu Istidraji, an saka masu. Suduniyar suka sani, ba su da sauran su koma wa Allah, tunda dai ba su yi masa qarya ba. To, amma ina ga mutumin da ya bude bakinsa ya ce shi ya yi imani da Allah, ya kuma ce ya yi imani da Manzon Allah, ya kuma ce ya yi imani da abin da Allah ya saukar wa Manzon Allah, amma a ayyukansa da zantukansa ya kangare wa Allah da kuma littafinsa, a lokaci guda kuma yana neman taimako
daga wajen wadanda suka yi wa Allah tawaye? A nan wanene babba? Da wanda ya yi imani da Allah da Manzonsa da littafinsa, amma ya kangare, yake neman taimako wajen Ibilis; da shi da Ibilis wanne ya fi ci gaba? Ka ga da ma Ibilis dan tawaye ne.
To ko, dole wanda ya fandare, ya kuma je wajen fandarraru yana neman gudummawa matsayinsa ya fi wulaqantuwa. Dole ne musulmin da ya sa kansa cikin wannan hali, kafiri ya fi shi, don shi kafiri bai yi wa Allah qarya ba.
Don haka ba mamaki irin qasashen da ake cewa sun ci gaba, suke take qasashe suna murjewa kuma suna tatse arziki su yi waje da shi, ana biye da su tare da kyakkyawan ikhlasi da bauta don su zo su ciyar da qasa gaba.
__________________________________________________
[Daga Littafin Nigeria Ina mafita Na jawaban Sayyid Zakzaky]
®__Mahadi__Tukur__Almizan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post