CIGABA DA FASSARSR KARATUB LITTAFIN AHKAMUL ISLAM FITOWA TA (5



CIGABA DA FASSARAR KARATUN LITTAFIN AHKAMUL ISLAM  FITOWA TA (5)

         WANDA MA'ASUMA NAGERIAN NEWS UPDATE TA SABA KAWO MAKU
     TARE DA MUDANSIR BARA'A MLF

Abaya mun tsaya .8. Ina ake magana akan shakku kan najasantuwar wani abu
       
Yau zamu tashi  a

9.ya haramta a najastar da takardar ALKUR'ANI da rubutun Sa ko kuma wani Abu da aka rubuta sunan Allah (t)ko sunan annabawa(as)ko kuma daya daga cikin  ahlulbat(as)idan daya daga cikin abin da aka ambata ya najastu,ko ya fada cikin wuri mai najasa ya wajaba a fitar dashi kuma a tsarkake shi nan take.

10.ya haramta a kebanta (tsuguno wato bayan gida)ana kallon fuskar  alkibla,ko kuma a fuskantar da gaban jiki ko abata baya kamar yadda ya haramta a kebanta a hanyoyi da lunguna Wanda basa bullewa sai da izinin masu wakafin wurin da kuma wuri mallakar wani ba tare da izinninsa ba a wurare wayanda aka bayar da wakafi ga mutane keban tattu kamar wasu makarantu na addini wayanda aka bayar  wakafi ga dalibai kebantattu na makarntar addinin an anharamta keban cewa a tituma hanyoyi da kofar gida da karkashin bishiya mai ya'ya da kuma wuri mai karfi(tsandauri) da ramukan kwari da ruwa musamman Wanda baya gudu kamar yanda aka haramta bawali a tsaye

Kubuta daga najasa aiki ne abin so ga maza fa'idarsa ita ce domin samun yakini a magudanar bawalinsa yadda ake yin(istibra'i)shine za ayi shafa da yatsa natsakiya daga mafitar ga'idi zuwa asalin azzakarin sa sau ukku sannan tun daga asalin al'aurarsa zuwa kan al'aurarsa zai matsa sau ukku sannan zai tatse kan al'aurar sau ukku.

Sati na sama zamu tashi kan fasalin MASU TSARKAKEWA
    Acikinsa akwai mazaje masu son tsarki kuma Allah yana son masu tsarkakewa

    Acikin suratul tauba aya ta 108.

Don karin bayani ko Gyara ko tanbaya zaku iya tuntubar wannan number 08166800005

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post