.NA TASHI DA WAQA TUN INA DAN PRIMARY!!!


Malam Rabi'u Nguru
.
```Acikin Shirin Filin Mawakan mu```

A firar da mukayi da Fitaccen Mawakin Nan *Mlm Rabi'u Nguru* a wannan Makon gata kamar haka:-

Daga *🌍MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE*

.
MA'ASUMIYYA: Allah shi gafarta, Masu karatunmu zasu so susan dan takaitaccen tarihin ka??
.
RABI'U NGURU ‘’To Mashaa Allah ni dai sunana Muhammad Rabi'u Ibrahim, an haife ni a cikin garin Nguru dake jihar Yobe a 14 ga watan Aprilun shekarar 1975, na yi karatun Primary da secondary duk cikin garin Nguru haka kuma nan muka yi wasu karatuttuka na littafai duk da cewa mun fita wasu garuruwa kamar su Kano duk don karatu. Kuma mun karatun haddar Al'qurani Mai girma a wata makaranta da ake kira Aliyu bn Abi Dalib dake cikin garin Nguru bayan wanda muka dan taba a Kano. Fannin karatun boko kuma na karanta Lissafi ne da Tattalin arziqi a matakin NCE a 2003 na zo kuma na karanta yadda ake sarrafa na'ura mai kwakwalwa.‘’
.
MA'ASUMIYYA: Al'umma sunajin waqoqinka sun banbanta da sauran mawaqa musamman yanda kake amfani da kalmomi na Hausa sosai a ciki shin daman kai cikekken Bahaushene kodai ka samu ilimin hausa na musammanne??
.
RABI'U NGURU ‘’Lalle ni Bahaushe ta bangaren Uba kuma ma ko ta bangaren mahaifya mahaifinta ne babarbare amma Mahaifiyar ta bahaushiya ce 'yar mutanen gaya.
Sannan kuma ina son nazarce na abinda nake da interest akai musamman wakokin Hausa tun ina dan karamin yaro a firamare na kan dauki littafai na wakokin Hausa na yi musu kari (launi) in ke rera kayana har na zo na tasirantu da wakokin su Alhaji Rabi'u Usman Baba."
.
MA'ASUMIYYA: A matsayinka na daya daga cikin manyan mawaqan wannan Harka, zamu so musan minene yaja hankalinka harka fara waqa??
.
RABI'U NGURU ‘’Kai!! Manya fa kace!!! 😃 Na'am kamar yadda na fada a sama ko lokacin yarinta ta ina da ra'ayin wakoki sosai don haka nema na kan bata lokaci wajen nazarce-nazarcen wakokin Hausa, kaga kamar wani littafin waka na Aliyu Namangi mai suna furen gero tun ina firamare nake karanta shi kuma nake yiwa dukkan wakar da na samu a ciki kari (launi). Sai dai kuma na tasirantu da wakokin yabon Manzon Allah (s.a.w.a) sosai wanda Su Sharif Rabi'u Usman Baba ke yi, don haka har yanzu za ka same ni ma'abocin jin wakokin sane, Sannan abin da ya ja hankali na fara yin tawa takaina, (kila haka mai tambaya yake son yace,) A kwai wata waka ta Bashir Dan Musa da nake ji ana sawa a gidan mu wanda yake cewa "YA,MUHAMMADU KA KUKA DANI A CIKIN MASOYA KASA DANI" to a cikin wakar akwai inda ya ke kawowa a cikin wani baiti ya ke cewa:
"--Na ji hadisin Nabiyyuna,
--Man madahali in ji Nabiyyuna,
--Walau bi naitin in ka zana,
--Sakamakon ka fa aljanna,
--Ka yarda na zana, nima ka yarda na zana ka san dani."
To wannan baitin ya ja hankalina sosai kuma gaskiya Allah ya amshi gibda ta ta nima in zana na yi wata waka kuma Shi Manzon Allahn na fara yiwa rubutun waka a rayuwa ta."
.
MA'ASUMIYYA: Yanzu kakai shekara nawa da fara waqa??
.
RABI'U NGURU "Na'am na fara waqa a 1989 wanda in ka lissafa yanzu za ka tarar kusan shekara 28-29 kenan.‘’
.
MA'ASUMIYYA: To yanzu Waqoqin naka zasu kai kamar nawa, kuma a ciki waccece ta zama maka kamar bakandamiyya??
.
RABI' NGURU "To da yeke a baya ba ma taskace su yanzu ne muke taskacewa, wadanda dai muke da su kuma mukan iya samun su a rubuce za su kai dari ko dari da wani abu.‘’
.
MA'ASUMIYYA: To ko zamu iya sanin waccece kamar Bakandamiyarka wacce Al'umma sukafi saninka da ita ko kai kafi jin dadinta a ranka??
.
RABI'U NGURU "Ba lalle bane ya zama wakar da al'umma su ka fi sanin ka da ita ya zama ita ka fi so ba, kaga Wacce al'umma suka fi sani na da ita itace fadi sosai wakar da nake kira LINZAMI DA WUTA.... Amma ni wakar da na fi so cikon wakokina ita ce JIHADI MAFITA.Sannan kuma wakar da na fu jin dadinta in ina rera ta ita ma daban take da wadan da na zano a sama ita wannan wakar itace NASIRUL MAHDI."
.
MA'ASUMIYYA: Zamu so kadan Rero Mana ita waqar JIHADI MAFITA mu dan jita ko baiti biyu??
RABI'U NGURU. "Na dan rero kona dan rubutu ?😃😃
.
MA'SUMIYYA: To kadan rubutu.
[1 In dan rero ko in rubuto?😃😃
[10:33am, 4/25/2018] Dan Masani: 😃
.
RABI'U NGURU "Amshi:
Haba Musulmi ba mu da Hujja in muka zauna ba mu yi Jihadi ba.
--Farko da sunan tabara Sarki Jallah maqagi na,
--Ka ji maqagin Rabi'u Allah shi yayi Abba na,
--Ubangiji mahaliccin kowa shi yayi mini Inna,
--Sannan yayi mini babban gata na Shugaba Babba.
.
--Ya Rabbi Sarki Ubangijina dubun salatin ka,
--Ka kara ninka shi khaliqina wurin Rasilin ka,
--Da Aalihi da sahabbai kamar su Aliyu Zakin ka,
--Da dukka mai son ya taka sawun Rasulina Babba.
.
--Bayan salati ga Musdafa 'yan uwa ku saurara,
--Duk dai da ni jahili nake kuma yaron cikin yara,
--Amma duk da haka 'yan uwa kun ga yaron ga ya lura,
--Ya gane ba mafita a kasar nan in ba jihadi ba.
.
--Don ko jihadin nan da kuk ji yana da tushen sa,
--Tun daga Rasulu Manzon Allah muka yo gadon sa,
--Yace duk in da ba a bin Musulunce a daura damarar sa,
--Don haka Manzo yayi kun san haka tu ba ahaifan ba.
Wakar tana da dogon amshi kuma tana da amshin ciki wanda ake bin baitikan da "TA'ALA."
MA'ASUMIYYA:
Akwai masu sha'awar zama mawaqa a wannan harka musamman matasa minene kiranka ko shawarinka a garesu??
.
RABI'U NGURU. "Haka ne a kwai.masu sha'awar zama mawaka a cikin matasan mu kuma tabnas ina da shawarwarin da zan ba su, ita wannan haraka ana yin ta ne don neman yardar Allah kuma wannan ahine asasin ta kaga kenan duk qanda yake da wata rawa davyake son takawa a cikin hatka a kwai bukatar ya sanya a fan shi cewa shima yardar Allahn yake nema sai kaga komai fes a gaban ka, amma in kai ka ji cewa yanzu kana so ne ka zama mawaki don ka zama kamar wane ko kuma ka fi wane to zao ai ta shan wahala a zuci da aiki sai kare hankoron ka a kokarin kamo wane ko wuce wane amma in ka ji cewa yqnzu ba fuskar kowa a gaban ka sai ta Allah sai ka zauna lafiya kuma shi Allah zai tsaya maka wajen kai ka inda ya fi dacewa da kai."
.
MA'ASUMIYYA: Minene kiranka ga Mawaqan harkan??
.
RABI'U NGURU. "Kira na ga mawakan harka shine su sake kara zage dantsen su wajen sauke nauyin da ya hau kan su na wayar da kan al'umma kan sani da kuma riko da hanyar Ahlul baiti, sai kuma kara zage dantse wajen amsa kiran Sayyid Ali Khamene'i na bayyana wa duniya irin Mazlumiyyar da aka yiwa su Sayid (H). Kuma zan so Mawaka su sako salo na sanar da ilmomi daban daban na abin da ya shafi Ahlul baiti ta sigar wake."
.
MA'ASUMIYYA: Minene kiranka ga wannan gwamnati bisa tsare Jagoran Harka Islamiyya Sayyid Zakzaky (H)da take har yanzu bata bashi 'yancin sa ba??
.
RABI'U NGURU. "To shi dai wannan tsarewa da gwamanati take yi tana yin sa me na bisa ka'ida na kuma kaga dukkan abinda da kae yin shi ba bisa ka'ida ba to kenan ba adaici ake ba kuma in ba adalci to zaluncine ke maye gurbin sa , to da wannan ne.muke cewa zaluncin da kae mana na tsare mana jagora ba bisa ka'ida ya ishe mu haka don yanzu tun muna nunawa al'ummar duniya ga irin zaluncin da aka mana harbtakai yanzu su suke nunawa ga irin abin da ka mana to kaga mu muna fadane ba fada ba amma muna kara jaddada musu cewa in tura takai bango tana sa akuya cizo. Ba zan rufa ba sai na kawo baitin wata tsohuwar waka ta lokacin Sani Abacha..
Bari in taqaita sunan wakar nan bazato,
Duk wanda ya jita to ya mini kyakkyawan zato
Ka fin in rfe bara na sanya fito na fito,
Ko.Gwamanti maza ta sau Imam Zakzaky ya fito,
Ko kuma wallahinduk mu yamutsa Najeriya."
.
MA'ASUMIYYA: Minene fatanka anan gaba, ko wani fata da yakamata Al'umma tasani wanda bamu tambayeka shi ba??
RABI'U NGURU. "To fatana dai bai wuce mu zama fi wujuhin Na'ima, ina nufin Allah ya dauwamar da mu cikin biyayyah ga jagora (H) ya kuma maida mu yadda yake so ya sanya karshen rayuwar mu shahadace."
.
MA'ASUMIYYA: Mun gode.
.
RABI'U NGURU. "Nima nagode"
.
Tare da
Salisu Umar Mazajen Zakzakyya
08021395846

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post