IMAM MAHDI (A.F) CIKIN HADISAN ANNABI (S.A.W.W) !!! ALAMOMIN TASHIN ALKIYAMA (9).

Daga Wakilin Ma'asumah Nigerian News Updates.

Tare da Ado Isa Guda.

(24)- Yin sadaqa/imfaqi ya zama tamkar haraji ne (tax). (Wato za a riqa yi ne dai bisa dole ba don son rai ba).

(25)- Za a riqa tsoron mutanen banza (mawaqan jahiliyyah da'yan siyasa) don jin tsoron harsunan su.

(26)- Fitowar Safiyani daga SHAM da kuma Yamani daga YAMEN (masu da'awar Annabta).
Daga Dama Sidi Munnir Sokoto, Sai Sheikh Adamu Tsoho Jos, kusa dashi Dr Sunusi Abdulkadir Kano, a karshe Malam Muhammad Abbare, shekaran jiya a wajen Muzaharar #FreeZakzaky a garin Abuja.

(27)- Kisfewar wata jama'ah a wani guri da ake kira Baida'ah tsakanin Makkah da Madinah. (Jama'ah ce wacce za ta fito don yaqar Ka'abah).

(28)- Yaqar wani yaro (Mahdi) daga iyalan Muhammad (S.A.W.W) a tsakanin RUKUNI da MAQAM (Rukuni Yamani da Maqama Ibrahim ).

A lokacin ne wani me kira daga Sama zai yi kira da cewa;

" LALLE GASKIYA NA TARE DA SHI DA KUMA MABIYANSA  .!"

Yace (Abu Ja'afar) ;

" Idan ya fito zai jingina bayansa da jikin Ka'abah, sai mutane 313 daga mabiyansa su taru zuwa gare shi (mataimakan sa). Farkon abinda zai fara furtawa ita ce wannan aya;

" BAQIYYATUL-LAHI KHAIRUL-LAKUM IN KUNTUM MU'UMININ  !" " Falalar Allah me wanzuwa ce mafi alkhairi gare ku in kun kasance muminai  !"

(Suratul-Hud, aya ta 86)

Sa'an nan yace;

" NINE FALALAR ALLAH, KUMA KHALIFANSA, KUMA HUJJARSA A KANKU  !"

Babu wanda zai sallama gare shi face ka ji yana cewa;

" AMINCI YA TABBATA A GARE KA YAA FALALAR ALLAH A DORON QASA  !"

Idan adadin mutane dubu goma (10,000) suka hadu a tare dashi, to, babu wani daga Bayahude ko Banasare ko kuma wani wanda ba Allah yake bautawa ba, face yayi imani kuma ya gaskata, sun kasance tafarki daya (1) tafarkin muslimci.

Wanda kuma ya kasance ba Allah yake bautawa ba, sai Wuta ta sauko daga sama ta qone shi."

(Nurul-Absar, Shafi na 278)

Mun kammala.

Yaa Allah ka sanya mu cikin mataimakan Imamul-Hujjah (A F)  !!!

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post