Sheikh Zakzaky @68 ADDININ ALLAH YANA SAKE TSUROWA NE.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates

Tare da Wakilinsu --Idishia Jos.

Wannan yunkuri da suke tatayi sai suga abin yadda yake basu takaici shine shi addinin musulunci ya bambanta. bugu da kari kuma sai suka ga addini yana sake tsirowa. Na'am akwai muhawala da aka yi daban-daban bayan da suka mallaki duniya.Akwai muhawalan da wasu
sukayi. Akwai wadanda sukayi muhawala na kokarin cewa ayi hattara dangane da mulkin mallakan bature, dasisa ne.

Yana nuna cewa ba ruwansa da addini , amma yazo fada da addinin ne. kuma har akwai wani littafi Wanda ake ce masa rayatul kubra,
Wata Sister a wajen Muzaharar #FreeZakzaky Jiya a garin Kano.
Ina jin har yanzu inada littafin, inba yana cikin abinda ya bace ba. Rayatul kubra su wadan da suka rubuta suna maganar ayi hattara dangane da
mulkin mallaka,tun lokacin mulkin mallakane.

Cewa fada yake da addini, harma yazama sukan tsare boda su tabbatar cewa shi wannan littafi baishigo nan ba, don kada ra'ayin yashigo nan.

Don daga Africa ta arewa ne da misra suka fara wannan da'awa din, kuma suka fara kakkama masu irin wannan da'awar suna kawar dasu. Harta hamada ma sun ringa binciken mutane su tabbatar irin wannan ra'ayin bai shigo nan ba. Kada muma yashigo mana nan, mufara cewa lallai ayi hattara da mulkin mallaka , ainihi kurace tazo da rigar akuya. wannan kamar ibara ce ta ingilishi, 'wolf' da gashin 'sheep'. wato idan Kura tasamu rigar akuya tasa, in ka ganta ga akuya , idan taje wajen awaki tana Meh, in dare tayi yaya kenan ? kun san me zatayi ? tasamu nama lafiya lau , tunda dama tashiga rigar awaki ne tazo ta kwanta. to barima muce cikin tumaki ta kwanta, don akuya ma wata kilama taita mata Ihu.

In tasa rigar tunkiya , ahali kurace , tazo aka ajiye ta cikin tumaki , in dare yayi kaga sai barna. to suna kokarin su nuna cewa lallai wannan kura ce da rigar tunkiya , karku karbe ta zama tazo tayi muku barna. Akwai wannan muhawalan.

A kwai kuma wani muhawalan bayan mulkin mallaka ya kafu daram daga cikin mutane daban-daban. alal misali, akwai muhawala na su 'yan ikwanil musulmin tare dasu hassan albanna , wanda shine ya assasa wannan da'awa din na cewa akoma addini , a lokacin da amisira aka dai na yin addini, susuka dauka kan su ya waye, sun zama turawa. a bisa gaskiya misirawa basu dauka su yan Africa bane, sun dauka su turawane . matansu nasa gajerun kaya cinyansu duk a waje matsattsu, kansu ba komai. Mazan su na zanzarewa irin na bature. su ala dole turawa ne suka zama saboda kansu ya waye . Ba'a yayin sallah ana ganin anci gaba. to yaki da turawa yasa suka fara tunanin ashe abin ba haka bane. Da sukayi yaki da isra'ila sai suka ga duk duniya, su sun dauka su turawane, sai yazama turawa duk sun juya musu baya , suka goyi bayan isra'ila. sannan sai suka ga wasu kasashe kamar na Africa, wadanda basu ganin su Africa ne, su suka maramusu baya. sannan ma yasa misira suka fara dan sassauci.

Amma mu misra, mutanen lalle tunanin su irin na turawa ne. Don a cikin nasihohin hassan albanna yanda cewa dan uwa ya Riga kula, yari
yin sallah sau biyar a rana, kuma yarin Ka yin azumin watan Ramadan; yana musu nasiha. Har lokacinda muka karanta muna mamaki, yaza'ayi hakan? suka CE Ai a misra zakasha mamaki, sai kaga mutum baya sallah, bayan azumi. kunsan mu anan lalacewar mu batakai haka nan bako ? har za'ace ana ma dan uwa nasihar ya rika Allah sallah sau biyar ? sai dai kace yakula da sallah din a lokaci misali, ko ya kula da yin salla din a jam'i misali, amma bazakace yarin ga yin sallah sai buhari ba, don dama yanayi.

Kuma da wuyan gaske, kodama kace Wani yanada sake da salla, to azumin Ramadan , akwai Wanda ba yayi anan ? asamu mutane ace surin Ka azumi fa. amma a wajensu ba mamaki, sai kaga mutum a wajen su baya azumin Ramadana sosai. wasu a cikin sittinoni suka je Sudan , sukace sai kaga a cikin ramadan mutum da rawani da rana yan sai da shayi kuma ana siye hard a Wani abin zaki. sai kagan su wai yara, kuna azumi, Ku yara? yaranku da Ku, yaro yayi azumi ? kai bala tsufaba kana azumi? zakaga wani shi ga shi ya girme ka , amma sai yace shi bai tsufaba, bazaiyi azumi ba. lalacewar takai salla da azumi, kamar ana ganin na Wanda Kansa bai waye bane.

Kuma zaran mutum ya fara koyon ABCD ,a boy and a girl shikkenan (ya zama bature ). Don akwai wani muna girmamashi yazo daga Sudan ne da rawanin sa ( bazan fadi suna sàba ) kuma yanda koyar damu, to kawai sai yafara koyon ABCD , a boy and a girl ,school." sai ya zanzare rannan, wai shi yayi, shikke nan.Ashe in mutum ya iya boko, shikkenan shi bature ne. sai gashi ran nan ya zanzare, ya ajiye rawani. Wata rana
da na gansa sai nayi masa làrabci, nace a'a Yaya? sai yayi min ingilishi, "I am now a lecturer ," Kansa waye kenan waishi yanzu laccara ne a jami'a , kamar shi yanzu nature ne. Ya dauka ya ci ga ba kenan. Akace ai su haka suke.

Ina kokarin in nuna maku mastawar lalacewa ga al'ummar musulmai takai ma su turawa sun dauka angama, sun riga sun mallaki duniya, kuma ya zuwa har abadan. Basu tunanin watarana akwai wani abu dazai dago. To, abinda yabasu mamaki shine juyin musulunci na Iran.

Wannan jawabin Sayyid Zakzaky (H) kafin gwamnatin Buhari ta afkamai a garin Zariya.

#FreeZakzaky.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post