""BATURE YA KAWO KAFIRCI NE QASAR NAN""


_FILIN JAGORAN GASKIYA_


""BATURE YA KAWO KAFIRCI NE QASAR NAN""


__Inji Sayyid Zakzaky (h)
Kun ga wannan ashe ya fito a sarari qarara, wanda duk zai ce kai ma, su ke amfana da kudin. Da za ka zama Gwamna ba barawo ba, da sun fitar da kai, barawon kawai suke so, saboda idan an saci kudin ina ake kaiwa? Can ake kaiwa, su suke amfana da kudin, sun kafa qasar ne don kansu ba domin mu ba.
Idan akwai wani Gwamna da zai ce ba zai yi sata ya kai Ingila ba, yanzu za a fitar da shi, a ce ba a ga amfanin gwamnatin tasa ba, gwamna kaza ya kawo kaza, shi bai kawo komai ba.
Wa ya ce ma sun kafa qasar domin mu ne? Sun kafa ta don kan su ne. Ka da ka ce min ai an samu ‘yanci da mulkin kai, abin da aka samu shi ne; da can shi Bature shi yake mulki da kansa, yanzu ya koyar da wadanda suka iya, yanzu su suke tafiyar masa da mulkin kamar yadda yake buqata.
___________________________________________
Ma'asuma Nigerian News Updates,
[Jawabin Sayyid Zakzaky (h) daga Littafin Mulkin Mallakar Turawa]
Tareda Wakilimmu,
©___Mahadi Tukur Almizan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post