_____BATURE BAI KAWO MANA CI-GABA BA!____


_Jawabin Jagoran Gaskiya [Sayyid Zakzay (h)]




__To, sai dai ita Nijeriya tana da nata matsalar, amma kafin na kawo ga nan, bari na zo ga cewa samar da qasa din. Ina iya ce mana, wannan magana da nake yi kyanta da a ce bara ne na zo na yi ta a nan, domin kuwa bara wancan, shekara biyu da suka wuce, lokaci irin wannan, ina jin a Disamba ne ko? Mun je garin Bormi, inda shi ne aka yi fafatawar qarshe tsakanin ‘yan mulkin mallaka da dakarun Sarkin Musulmi na wancan lokacin Attahiru (Attahirun Amadu), wanda suka kashe mutane da daman gaske ciki har da shi Sarkin Musulmi din, shi Attahiru din da ‘ya’yansa da wadansu mutane, suka yi ma abin da ake ce ma Dala din nan da gawarwakin wadanda suka karkashe kafin su tabbatar da ikonsu.


To, shekaru dari (100) bayan wannan, domin sun yi shi a 1903 daidai. To da shekara dari suka cika, a 2003 kenan, ‘yan uwa sun yi taro na qarawa juna sani, sashen ‘yan uwan da ake ce ma ‘yan ‘Academic Forum’, wanda galibansu Malaman Jami’o’i ne da kuma dalibai, sai suka shirya Semina a can garin Bajoga, wanda ke kusa da Bormi din, yanzu Bormi ta zama kango. Ko da yake yanzu garin Bajoga kamar shi ne Bormin, dama su ‘yan Bormi din ne suka dawo Bajoga, dama kuma tsakaninsu ba nisa, kamar dai wuri daya ne kawai.

 A wancan lokacin sai muka je aka yi bikin cikar shekara dari (100) bayan kafuwar ‘yan mulkin mallaka da kawo qarshen gwagwarmayar
Attahiru.To kuma, mun ziyarci shi qabarin Attahiru a lokacin cika shekara dari din, kun ga yanzu shekara dari da biyu kenan(102). Na san a maganar da na yi a can na fadi abin da ya faru a nan birnin Lokoja a watan Afril na 1904, wanda yake su mutane suna ganin cewa kamar Bature ya zo da adalci ne, ya kuma samar da qasar da bata, ya kuma samar mana da harshen da da ba mu da shi. Kila ma ya ba mu ilimin da da ba mu da shi.To, amma kila suna kallon abin da suke son su yaba masa da shi ne kawai.

Amma akwai wani abu guda, Bature bai zo qasar nan saboda mu ba! Wannan tambayi kowanne Bature zai iya gaya maka haka. Bai zo qasar nan saboda mu ba, bai zo domin ya wayar da kan masu duhun kai ba, bai zo domin ya kafa qasa ta ci gaba ba, bai zo domin ya kyautata rayuwar mutanen da suke wannan wurin ba!Bature ya zo ne domin qashin kansa! Ya zo sata ne!
Barawo ne dan fashi! Ya zo ne ya dibi arziqi ya ci-gabantar da kansa, ya kuma sallaxa ikonsa akan mu, kuma ya bautar da mu bautar dindindin! Wannan, abin da ya kawo Bature kenan, kuma har yanzu zancen kenan.

Idan da gaske ne Bature ya raba wasu (mutane) da turbude ‘ya’yansu tagwaye, ko kashe ‘ya’yansu tagwaye, kuma ya kawo ma wasu sutura don da suna tafiya tsirara, kuma ya kawo ma wasu ilimi don da ba su iya rubutu da karatu ba. To, mu Bature bai zo mana da ko daya daga wadannan abubuwan ba! Bature bai kawo mana riga ba, don muna da rigar da ta fi tasa, don na shi gajeren Wando ne da ‘Shirt’ da Malfa, illa iyaka.(Bature) yana bayan-gida ne a bokiti.

Mu bai zo mana da gini ba, bai zo mana da sutura ba, uwa-uba, bai zo mana da ilimi ba! Ya zo ya samu dama muna da ilimi, ya kuma zo ya samu muna da sutura, ya samu har walayau muna da nizami na rayuwa da kuma tsarin hukuma.
Shi bai kawo mana ko daya daga cikin wadannan abubuwa ba!Amma ban ce muku bai kawo ma kowa ba, don da gaske ne ya ba wasu.

Har walayau idan Bature ya kawo addini, to ya kawo ma wasu addinin ne, mu ya kawo mana addini ne? Da ma ya same mu muna da addini, saboda haka Bature bai kawo mana addini ba.
Amma da gaske ne ya kawo ma wasu addini, ya kawo ma wasu riga, ya kawo ma wasu ilimi, amma mu bai kawo mana ba! Saboda muna da addinin da ya fi nasa, muna da ilimin da ya fi nasa, muna da suturar da ta fi tasa, muna da al’adar da ta fi tasa. Saboda haka mutum ya hade mu gaba daya, ya ce; ai duk cikarmu gaba dayanmu abu daya ne kafin Bature ya zo, bai mana adalci ba. Domin duk cikarmu gaba dayanmu ba abu daya muke ba, muna da bambanci!

Saboda haka a yau idan wani yana da kwadayin addinin Bature, da ilimin Bature, da suturar Bature, da tuwon Bature, da al’adar Bature, sai mu ce; mu wadannan abubuwa muna qyamar su ne, har yanzu ba mu gushe ba muna qyamar su.
 Saboda mene? Bature shi dai ba Musulmi ba ne, kuma uwa-uba ya ma zo da Kafirci ne, shi ne kuma wannan abin da mutane ba su lura ba.
     ___________Zamu cigaba Insha Allah__________

Ma'asuma Nigerian News Update,
[Littafin Jawaban Sayyid Zakzaky (h) MULKIN MALLAKAR TURAWA]
Wakilinmu,
®__Mahadi__Tukur__Almizan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post