TAKAITACCEN TARIHIN IMAM HUSAIN(AS)


      DAGA MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE TARE DA Khadija hamza Malumfashi



Bismihi Ta'ala

Anhaifi imam husain a ranar alhamis uku ga watan sha'aban shekara ta sittin da hudu bayan hijira a cikin garin madina.
  Sunan mahaifinsa Aliyu ibn Abi dalib sunan mahaifiyarsa fatima diyar manzon Allah.Anayimasa alkunya da Abu abdullahi sannan anayimasa lakabi da sayyidush shuhada'u.

    Imam yanada yaya bakwai hudu maza uku mata.

  Imam yana da  falaloli da dama manzon Allah yana cewa ni daga husaini nake kuma husaini daga ni yake,sannan yana cewa Hassan da Husaini alkhairin mutanene a bayana da kuma bayan mahaifinsu,sannan yaqara da cewa Hassan da Husaini sune shugabannin samarin aljanna.

  Imam yakasance mai yawan ibada a rayuwarshi yakasance yana yin sallah raka'a dubu aduk rana,yakasance me yawanyin azumi,sadaka dakuma karatun al qurA'ani.

  Daga cikin kyawawan dabi'unsa yakasance me hakuri da irin kowace musiba data sameshi,yakasance me yawan yin sadaka dasauransu.
 

   Imam yayi shahadane aranar goma ga watan almuharram ranar juma'a a wata ruwayar ranar asabar.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post