MAFI WAHALAN ABU GA IYAYE SHINE TARBIYAN YARAN SU.





Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates

Ya dana ka tsaida sallah kayi umarni da mai kyau kayi hani da mummuna, kuma kayi hakuri game da abin da ya same ka kuma lalle
wannan yana daga muhimman al'amura kuma kada Ka karkata fuskarka ga mutane kuma kada kayi tafiya a cikin kasa kana mai nuna
fadin rai. Kuma lalle Allah baya son dukkan mai takama mai alfahari. Kuma ka tsagaita a tafiyar ka, kuma ka runtse ga sautin ka, lalle mafi
munin sautika hakika, shine sautin jakuna." (31:17,18,19).

Daya daga cikin muhimman ginshikan al'ummar dan Adam shine iyali,wanda ya hada Da da UBA da UWA da kuma 'YA'YA. kamar yanda
dan Adam ke girma- yakuma kai ga kamala ta irin wannan hanya al'umma zata kai zuwa ga kamala. Saboda haka ne aka kaddamar da
cewa iyalai sune mafi muhimmancin kusoshin cigaban al'ummah. Kuma bugu da kari saboda haka ne musulunci yabada muhimmanci game da iyali, yakuma tanada ka'idojin musamman domin iyalin.

Iyaye su ke da alhakin tarbiyan yayansu, saboda haka sai su shirya su dauki wannan nauyin kafin yin aure da bayansa. Nauyin iyayen ba wai
kawai ya shafi ciyar da shayar da tufatar da yayan bane, haka ma alhakin su ne su gyara zukatan yaran su kuma yi musu tarbiyar motsa
jiki da kyautata hali da kuma iya zama da jama'a. Kuma a koda yaushe su zamo suna jagorantar yayansu ta kowannane fanni. Iyaye sune farkon abin koyi ga da, ta hanyarsu dazai san mecece rayuwa, kuma ya san me zaiyi da yadda ya kamata ya zamo in ya girma.

Saboda haka tunda 'ya'ya suna waiwayar iyeyensu ne wajen tambayoyi da kuma neman shiriya to lalle ne iyaye su zamo su kansu masu
tarbiya. Lalle ne su nuna misalin kare gaskiya, su kuma kiyaye girman kai domin su nuna kyakkyawan halai. Domin bazai yuwu iyayen banza suyi wa 'ya'yansu tarbiyar kirki, koda sunso hakan.

Sai dai idan iyayen suna son su yiwa yayan tarbiya kwarai to su akan su sai su zamowa 'ya'yan nasu abin koyi ta hanyar kyautata hanyar
mu'amalarsu, kamar cin abincin su da barcin su da sauransu. Wani nauyi kuma da yake kan iyaye shine su samar da dangantakar gaskiya
da kyautatawa a tsakanin su saboda wannan yana sa yara su girma da mutunci, kuma su san abin da ya kamata sukuma zamo abin sha'awa
ga kowa, mazan su da matansu. Idan iyaye suna zaune tare cikin soyayya da kaunar juna suna kuma kyautatawa juna to wannan kyakkyawan darasi ne ga yara yanda zasuyi zama na gari zuwa ga ba. Dabi'ar uwa darasine ga yar ta idan yayi aure nan ga ba, dabi'ar uba kuma darasine ga dansa yadda sai tafiyar da iyalinsa nan gaba.

Iyaye dai sauke da alhakin tarbiyar yayansu a dukkan fannonin rayuwa. Saboda haka yakamata su Gina rayuwar yara su ta yanzu da kuma tanan gaba tazamo mai anfani da farin ciki. Babu shakka idan cewa iyaye suka ayi watsi da wannan tarbiya sunyi Babban laifi domin kuwa saboda rashin tarbiya ne ake keta mutuncin bil'adama a guraren da babu wanda ya damu da Wani.

Saboda muhimmacin samun jama'ar maza da mata da ba lala tattuba shiyasa ya zamo idan idan iyaye sunyi watsi da tarbiya, to wasu da suka ce su suyi tarbiyar yaran. Neman ture rashin adalcin da akayiwa mata a da, sai kuma aka shige gona da irin. Idan da turawa zasu fara wannan yun kuri da kafa doka a yau, zasuyi hankali fiye da shekaru darin da suka shige. Wani binciken da akayi danga ne da halayen mutum da dabi'arsa, yamuna cewa wasu daga cikin wadannan nazarori da aka dauka sunyi sunyi gaggawa kwarai kuma ba dai dai bane.

Wannan mushkila ce guda, Wani raunin da ake cikin dokokin turai dangane da hakkin mata, Wanda yake shine jahilcin su daga ne da
gwargwadon da bukatun maza da mata. Dalili na biyu kowa da yasa dokokin turai dangane da mata suka zama nakasassu, shine rashin gaskiyar masu kira da manufar shugaban ni
masu naiman daidaita maza da mata.

'Yan Adam suna zama mutanene kawai ta hanyar tarbiya da kuma ilimi. Idan mutum ya girma a gurin da ya dace to zai zamo mai anfani kuma mai kima, haka kuma inda zai tashi a gurin da bai daceba kuma aka samu jinkiri sake masa tarbiya, to zai zamo mai cutarwa ga kansa da kuma al'ummarsa. To yanzu zamu dubi wannan muhimmin abu ta hanyoyin tarbiya daban daban a musulunci.

Miji yana da wasu hakkokin mata da suka rataya a wuyansa, haka kuma matar, dukkansu kuma sunada wasu hakkoki na yayansu daga
rataya a wuyansu. A kebance uwa na da Wani muhimmin nauyi na musamman na tarbiyan yara da yahau kanta. Dabi'arsa itace mai nuna
matukar tarbiyar da ya samu. Saboda haka idan da za'a bar yaro a cikin dabbobi a daji harya girma to ko shakka babu to zaitashi dawasu halaye irin na dabbobi.

Daga wakilinsu Idishi Jos.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post