Yadda ake Gane Son Fateemah…

YADDA AKE GANE SON FATIMA (AS) 



To muna iya tambayar yaya ake yi,a yi so ne ma tukuna? Ko da mu qaddara kana son babanka ne, sai ka ce ya baba ina son ka, shi  kenan kana son sa kenan? An gama. Mu qaddara in ya ce ka yi abu, ba za ka yi ba, in ya hana ka ba za ka hanu ba, kana ma yin abin da ba ya so, sai kuma ka ce ya baba ina son ka. Ka ga muna iya cewa in dai da gaske ne kana son Mahaifinka, to za ka so ka yardar da shi ne, ka guje wa abin da ba ya so. Wannan shi ne daidai. Haka kuma duk wanda yake son wani zai yi kokari ya yardar da shi ne, ya yi masa abin da yake so. ya guji abin da ransa ba ya so. Haka son Manzon Allah yake. Akan ce ana son sa ne kawai da fatar baki? Ko a yi waka a yabe shi an gama? Ana bin abin da ya zo da shi ne, a rike abin kam-kam, shi ne an nuna masa qauna. A misaltu da abin da ya ce, a hanu daga abin da ya ce. Ballantana kuma har ya ce ga wannan abu shi yana son sa, sai ya zama wani ya ce yana son wannan, ka ga yaya kenan? Saboda haka idan aka ce wanda ya so Fatima, to tambaya za ta taso; yaya za ka so Fatima? In da ko abin da za ka so ta sosai, abin da ya fusata ta, dole ka yi fushi da shi. Ko kuma in ce wanda ya ba ta haushi, dole ya ba ka haushi, makiyinta dole ya zama makiyinka. Ba yadda za a yi ka ce min kana son Fatima, a zuciyar da kake son ta kana son makiyinta. Karya kake.

Kamin kaci gaba da Karatu KASANCE DAMU A FACEBOOK: - Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update

Da za a ce maka alal misali wannan Sayyidah Fatima din nan da kake so, a ce akwai wani ya zage ta, ai a nan take fuskarka za ta canza. Za ka fusata. Ya zage ta? Sai aka ce maka akwai wani ya wuce nan ya gaya mata mugunyar magana, dole hankalinka ya tashi. Da ba don Allah (T) da rahmarsa yana rike sama da qasa ba da sun rugurguje sakamakon an jingina masa da. Akwai wata qissa da nake karantawa dangane da Annabi Isa, yana fassara wata aya, sai ya ce wannan aya da za ka bi zahirinta kamar tana nufin kaza kenan, amma ba haka take nufi ba. To sai ya fadi magana din, wanda yake magana din ta girma, sai da kasa ta girgiza a lokacin, kun ga fa Karamar magana kenan. Ba muna ba da misali ne ba, ba mun ce haka ne din ba. Kamar yadda Allah yake cewa sama da qasa daf suke da su tsage don sun jingina wa Allah da.
Ka san idan aka jefo wata magana, ko wani abu ke hannunka sai ka jefar saboda ka firgita, abin za ka ji ya ratsa ka ne kamar an yi maka tsawa saboda nauyin abin. Shi ya sa kiyaye mutuncin Annabi ya zama kiyaye addinin gaba daya. Da wani zai wurga wa Manzon Allah wata magana, to sai kaji an yamutsa ka, kamar yadda naji wani Malami yana fadin cewa ai idan ta kai ma an zagi Annabi mutum yana iya haukacewa. Zai iya haukacewa a lokacin, ya kasa mallakar kansa ko meye ya faru. Kuma ai mutane sukan nuna a kan abin da suke so. Ba ka ganin zumudinsu a kan wani, har ana rike wani. Akwai wani wai an zagi Gwamna, ana ta rike shi wai zai kai duka. Wai don me za a zagi Gwamna bawan Allah wanda yake shari’a? Kuma ma ba a zage shi ba, an ce ne ba shari’a yake ba. Sai ka ga irin wadannan abin mamaki fushinsu a kan me ya karata idan aka zagi Annabi, wanda yake nufin a zuciyarsu al’amarin Annabi ya mutu murus, shi ya sa, A kan wani abu ko za ka ga sun harzuqa.
In da an ce ka san kimar Manzonka, ka san kuma qimar da ya ba ’yarsa har ya zamana sonta sonsa, qinta qinsa, to da ko wani in aka ce maka ya yi wa ’yar wani abu da ko za ka damu. Kai ko Sarkin gari ne ya mutu, mu kaddara bayan da Sarkin garin ya mutu. sai Wazirin gari ya mari ’yar Sarki, ya kake tsammani tsakanin sa da Sarkin kafin ya mutu? Masoyin Sarkin ne? Tunda in da Sarkin zai dawo ba zai mari ’yarsa ba ko? Ko zagin ta ba zai yi ba. To ballantana a ce maka wannan Sayyidah Fatima ba wani ya zage bane, wani ya mare ta. Kai! Ai ko abin ya girmama.
Akwai wani yake ce min. mun yi musharaka da shi ne a aikin hajji. shi asalinsa mutumin Labanon ne. amma da yake ya yi shiga irin ta Malamai, sai wani direbansa ya dauka mutumin Iran ne, sai ya yi masa irin gagaliya din nan, ya ce kai mutumin Iran ne? Ya ce eh. Me ya sa ba ku son sahabbai? To da yake shi Balarabe ne, ya iya Larabcin sosai, kila da mutumin Iran ne bai iya Larabci ba, ba yadda ya iya da shi, sai ya ce masa kai wane irin mutum ne? sai ya ce shi Khuzaifi ne, da yake Larabawa suna da wasu kabiloli. Sai ya ce har ka san wannan ne? Ya yabi babansu Khuzaif. Sai ya ce kamar misali babanku Khuzaif ya ga cewa zai mutu ya ce a kawo takarda da alkalami zai rubuta maku wani abu, yana so ku Khuzaifawa ku rike shi bayan ba shi, sai wani ya hana, har baban naku ya mutu bai bar muku wannan bayanin ba, yaya tsakaninka da shi? Sai ya ce ai in na gan shi sai duka. Sai ya ce oho, to ka ga irin wannan wasu suka yi wa Annabi. Sai ya ce wa ya yi wa Annabi haka nan? Sai ya ce je ka tambayi Malamanka.
Mu qaddara kuma har wala yau wannan Sayyidah din wadda sonta ke tare da son Annabi, wani ba marinta ma ya yi ba ya ce zai qona ta da wuta, ya kuma zo da wutar. Ka ga ta nan ne zaka nuna son Fatima in da gaske ne. Ta nan ne fushinta zai kasance fushinka, kuma masoyinta masoyinka, kuma makiyinta makiyinka. A nan ne za ka nuna so din. Amma karya za ka yi ka ce min kana son Fatima alhali a zuciyarka akwai tausayi ga makiyinta. In kana tausayin makiyinta da kun yi zamani da ka zama masoyinsa. Da ko haka nan ne, kila da kaima da kai aka yi wannan aika-aika din. Ai akwai wasu da suka ce mana, da bakunansu suka fada, abin ya ba mu mamaki, rutsawar da aka yi mana a Jami’ar Bayero, wasu cewa suka yi “Za mu kashe ka kamar yadda aka kashe Husain a Karbala.” Har wasu cewa suke “Nan ne Karbala.” Sai nake ga wannan shi muraran ya fadi abin da ke ransa, kuma tabbaci hakikan da ya yi zamani da Imam Husain lokacin waqi’ar Karbala, to da lalle yana tare da Yazidu, tunda har ya yi furuci da shi a halin yanzu. Gwanin ban mamaki.


Mai karatu wannan wani yanki ne daga cikin jawabi na hudu da su  ALLAMA SHEIKH  Ibrahim Alzakzaky (H)  suka yi a jerin jawaban da sukanyi a makon Zahra. Wato wannan jawabin da suka  yi a shekara ta 2001 a zauren taro na kongo Zariya. 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post