TABBATAR ADDINI DAGA BAKIN SHEIK IBRAHIM ZAKZAKY (H). A Shekara ta 1990,Kashina [03].

@Isma'il Abubakar Idris Katsina.

Cigaban Jawabin Sayeed Ibrahim Zakzaky mai suna ( TABBATAR ADDINI ) wanda yayi a shekara ta 1990.

Harkar Musulunci ta Allah ce, Allah na tabbatar da wanda yaso akan Addininsa, da gudumuwarka ko babu gudumuwarka Idan Allah yaga dama zai iya kawar dakai yayi amfani da waninka wajen tabbatar addininsa.

Hassadar Iblis ga Annabi Adam bai sa Allah ya fasa halittar Annabi Adam ba!, idan kayima Harkar Msulunci hassada kaje kaita hassadar ka duk hassadarka bazaka kai Iblis ba!.

Domin da Iblis yayima Annabi Adam sujada kamar yadda Allah ya umurceshi da yasamu daukakarda tafi ta Annnabi Adam, Addini Musulunci na Allah ne, mukuma kayan Allah ne, Allah ne zai tabbatar da addininsa da wadan da yaga damar Tabbarwa.

Idan mutum yana ganin cewa Harkar Musulunci kira ne na Allah amma yana tunanin cewa masuyin wannan kiran basu can-canci suyi kiran bane to ga kule ga masu irin wannan tunanin, " idan akwai Wanda suka can-canci suyi wannan kiran suzo suyi kiran akwai wanda ya hanasu ne", munyi kira a dawoma addini Allah sai ace bamu can-canta muyi wannan kiran ba.

Bamu dauki can-canta ko girma muka dorama kawukanmu ba, munsamu kanmu cikin wani mugun hali na kin bin addinin Allah wanda mukasan cewa inmun koma ga Allah zamu samu uzrinsa da rahamarsa tare dabin hukunce-hukencen littafinsa Alqur'an mai girma shi zamubi musamu Uzri Duniya da Lahira.

Idan akwai wani zamanin da za'ace baza'ayi aiki da Musulunci ba to da Allah bai aiko Annabi Muhammad a matsayin dan Sakon karshe cikin Annabawa ba, addinin musulunci zai aikatu daga wannan zamanin harzuwa lokacinda za'abusa kaho saidai in mutum bazai iya aiki dashi ba.

Komin lalacewar Al'umma idan sukaso komawa ga addinin Allah zasu koma akoda yaushe, domin addinin Allah yana nan baya lalacewa har'abada Allah yayi alkawalin kare addininsa.

Allah ya yima Annabi Muhammad Alkawali cewa komin Lalacewar Al'umma baza'arasa wanda zaiyi kira abi Allah ba.

Sheik Ibrahim Yaqub El- Zakzaky acikin Jawabinsa na 1990 mai suna " Tabbatar Addini "

           Munhadu Kashi na (04).

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post