Sahabin da aka Kora daga madina saboda fadar falalar ahlulbaiyt.


Daga MA'ASUMA Nigeria news update

Alkalamin Wakiliyar mu Sakina Ahmad Kazaure m.s.n 006)

ABUZARRIL GIFFARI-:Sunan sa na asali shine jundub bn junadata, dan kabilar gaffar ne, shine dalilin dayasa  ake cemasa Al-gaffari. Tarihi bai tabbatar da lokacin da aka haife shi ba, sai dai abinda yake abayyane shine an haife shi da shekaru masu yawa kafin bayyanar musulunci saboda lokacin daya rasu Ya tsufa sosai.
   
 Dangane da abinda Ya shafi musuluntarsa kuwa malaman Tarihi sun tafi Kan cewa Yana daga cikin na farko- farkon musulunta Don ance shine na hudu ko na biyar cikin wadanda suka fara musulunta.
 
 Abuzarr dai an sanshi mutum ne  da aka sanshi da jarumta, don kuwa alokacin duk wanda Ya musulunta to yana boye imaninsa ne saboda gudun cutarwa. Amma Abuzarr Ya fito fili ne a dakin ka'abah tare da sanin cewa duk kafiran makka suna gun Ya bayyanar da kalmar shahada.
 
 Sanarwar da Abuzarr yayi tana a matsayin bude shafi na fuskantar gumaka da azzaluman shuwagabanni na lokacin, bayyanar da musuluncin sa kuwa keda wuya sai jama'a suka fadashi da duka wasu suna zaginsa, sai dai duk da haka bai fasa fadin *laaaa ilaa ha illallah Muhammadur-rasulullah* ba. Haka suka ci gaba da azabtar dashi har lokacin da wani daga cikinsu ya kwace shi ta hanyar fadawa kuraishawa cewa idan kuka kashe shi to kusani Akwai yiyuwar yan kabilarsu zasu dauki fansa. To atakaice dai bayan wannan bara'a ta Abuzarr sai Ya tafi wurin manzon Allah (s.a.w.w) don ci gaba da samun koyarwa da tarbiyar musulunci.
 
  Abuzarr bayan imaninsa yaci gaba da rayuwa da manzon Allah (s) har zuwa lokacin hijra,inda bayan komawarsu madina yaci gaba da rayuwarsa ne a masallacin manzon Allah (s) tare da sauran sahabbai marasa abin hannu wanda akafi sani da as'hab al suffa. Abuzarr Al-gaffari Ya halarci wasu yakoki tare da manzon Allah (s) sannan kuma Ya halifanci ma'aiki a garin madina lokacin fita wasu yakoki.
   
 Abuzarr Al-gaffari Ya kasance yanada matsayi Mai girman gaske musamman a wurin mabiya ahlulbaiyt (a.s) Don harma Ya kasance suna kiran Abuzarr da mikdad, Salman, ammar da suna arkanul arbaa( rukunnai hudu).
 

Ni Sakina Ahmad yayin danake karbar Kyautar da Shafin Ma'asumah Nigerian... Yayiman a garin katsina wajen Taron karawa juna sani da akayi a 2-3-2019


 Ruwayoyi da dama daga imamai suna nuni da irin matsayin Abuzarr dama kiran mabiyansu dasuyi koyi da ayyuka da Dabi'unsa bama shi'a kadai ba har sauran musulmai ma suna girmamashi.

   Bayan wafatin manzon Allah (s) Abuzarr Ya kasance tare da imam Ali(a.s), Abuzarr yakasance mutumne mai gaskiya da amana, sannan Yana kyamar zalunci, hakanne yasa Ya dinga samun matsala da mahukunta a lokacin halifanci usman, kai harma da shi kanshi Khalifa din, musamman yadda ake gudana da al'amarin baitul mali, da fifita dangi Dana kusa, Yana kuma kawo hadisai na falalar ahlulbaiyt aduk inda Ya kasance, irin wannan dabi'a da halayya tasa tasa aka koreshi daga garin madina zuwa sham, to sai dai acanma Abuzarr baiyi shiru ba, duk kuwa da kokarin rufe bakinsa da akeyi ta hanyar bashi cin hanci. Koda yake daga baya an maidashi madina wai Koda bakin sa zai mutu sai dai kuma kash!! I hakan bata yiyuba.

    Daga karshe dai aka sake turashi hijirar dole zuwa wani waje da akecema *rabaza* don a rabashi da Jama'a. Alokacin fitowar sa daga madina zuwa *rabaza* daga cikin wadanda suka rakashi Akwai Amirulmuminin Ali (a.s) da yayan sa imam Hassan da imam hussain (a.s). Haka Abuzarr da Mai dakinsa da kuma yarsa suka tafi wannan hamada ta rabaza da bakomai a wurin Don fara sabuwar rayuwa ta azabtarwa sakamakon fushin khalifan zamaninsa.

Haka Ya tabbatar da fadin manzon Allah (s) cewa: Allah yayi rahama ga Abuzarr Yana rayuwa shi kadai, zai mutu shi kadai, kuma za'a tayar dashi shi kadai, sannan wasu muminai zasu kasance tare dashi.
 
   A karshe yayi wafati sakamakon irin mummunan yanayin da aka sashi a ciki dama munin inda aka kaishi, yasa ciwon dayake tare dashi yayi tsanani, ga tsufa haka ma iyalansa sun kamu da wannan ciwo da yayi sanadiyyar rasuwar su.

     Amincin Allah Ya tabbata a gareka Ya Abuzarr Al-gaffari ranar da kayi wafati da ranar da za'a tashe ka a matsayin wanda aka zalunta.


 Daga *Sakina Ahmad Kazaure.*

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post