TABBATAR ADDINI DAGA BAKIN SHEIK IBRAHIM ZAKZAKY (H). A Shekara ta 1990 . Kashi na [02]

Isma'il Abubakar Idris Katsina. 

Cigan Jawabin Sayyeed Ibrahim Zakzaky na 1990, Shekara 29 data wuce. mai suna "Tabbatar Addini" Kashi na (02).

Lokacinda turawa suka fahimci Al'umma zasu koma ga musulunci sai suka fara kira akan cewa Addinin Musulunci ba addini bane, sunfara rarraba kan Musulmai.

Turawa sunRarraba addinin Musulunci akida-akida tare da daukema al'umma musulmai hankali akan addinin musulunci alokacinne wasu kungiyoyi na Musulunci suka kunno kai ko'ina an rarraba Musulmai biyu, an rarraba masallatai anazaki Musulmai na farko dana yanzu.

Lokacin da Harkar Musulunci na kunno kai sai Al'umma suka fara cewa a'a wanna kiran na Harkar Musulunci shima kungiya ne. Sayyeed Zakzaky ya basu amsa yace " a'a Harkar Musulunci ba wata kungiya ba ne, wannan addininnne wanda manzon Allah yazo dashi".

Kada Al'umma suyi tunanin cewa Harkar musulunci kungiya ce mai Hedi kwata wani waje daban, kada Al'umma suyi tunanin cewa Harkar musulunci nada Sakataren watsa labaru da Gwamnoni da oganayizas ko tanada Wa'azin Kasa da Kaza a'a, Harkar Musulunci addini ne ba 'yanbaruwanmu da addiniba. Mu 'yan ga addini ne.

Babu wata Rijista da akeyima addinin Musulunci tunda aka haifi mutum da rijistar sa duk wanda ya shaida da "La'ilaha'illalahh Muhammadu Rasulillah" ya yi rijista. Duk wanda yace Harkar musulunci kungiya ce a tasa  fahimtar to kungiyar ce sunan kungiyar (Musulunci, sunan 'ya'yan kungiyar " Musulmai").

Wannan lokacine na dawo da addinin Musulunci zakasha mamaki idan kaji yawan adadin Mutanen da suke shiga addinin musulunci musamman Amerika da Ingila.

Allah yace " zantabbatar da addinin Musulunci koda kafirai sunki", Azzaluman Duniya cikinsu ya 'Duri ruwa wanna lokaci ne na dawo da addini Musulunci.

Allah yana cewa "farkon Kowane karni zantada wani Mujaddadi wanda zai farfado da Al'umma ta zuwaga addini, yanzu muna Farkon karni na (1410) daga nan kafin rabin karni angama komi da yardar Allah.

Matakan da ake bi dan cimma nasarar da'awar Harkar Musulunci, masuganin addinin Allah bazai tabbata a Najeriya ba ga amsa÷ ko kaki ko kaso Addinin Allah zai tabbata a dorun Duniya. Allah ne zai tabbatar da addininsa.

Kana da tantama kan  cewa Allah ne ya halicci sama da kasa, ya halicci Mutum da Aljani..?. Kana da tantama kan cewa Allah ne zai Tabbatar da addinin Musulunci ko damu ko babu mu.

       Muhadu Kashi na (03).

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post