'YAN SHI'AH KUNA GAGGAWA NE!!

NASARA FA NA NAN TAFE !!!

Ku qara haquri da juriya kawai, ai tunda kuka kama wannan hanyar dole ku gamu da abinda kuke gani. Yanzu mu da ba irin hanyarku muka kama ba, me ke faruwa damu?

Muna yin wa'azin mu ko ina, kuma a duk inda muka so, amma tunda muna tare dasu kuma ba mu nuna musa muna so mu qwace abinda ke hannunsu (mulki) ya dawo hannunmu ba, ai babu ruwansu damu. Ko Fir'auna ma da kuka ga yayi yunqurin halaka Musa (A.S) saboda ya zama masa barazana ne ga mulkinsa da kuma rayuwarsa.

SHIGA NAN DOMIN KAYI LIKE DIN SHAFIBMU NA FACEBOOK: Ma'asumiya Facebook

Tunda mu ba za mu iya yin abinda kuke yi ba, ku kuma imaninku ya kai haka, za mu qarfafe ku da wani hadisi da yazo cikin babban littafinmu kamar haka;
Bukhari ya riwaito cewa, Muhammad Bn Musannah ya bamu labari, Yahya ya bamu labari daga Isma'il; Qais ya bamu labari daga Khabbab Bn Arrat yace;
Mun kai kukanmu ga Manzon Allah (S.A.W.W) (saboda tsananin cutarwar da ake mana), lokacin yana kishingide kan shimfidarsa cikin inuwar Ka'aba, muka ce masa;
Yanzu ba za ka nema mana taimako ba? Ba za roqa mana Allah (ya kawo mana qarshen wannan zalunci) ba? Yace;
" MUTUM YA KASANCE CIKIN WADANDA SUKA ZO GABANINKU, ANA TONA MASA RAMI A SANYA SHI CIKI (zuwa qugunsa), SANNAN AZO DA ZARTO (handsaw) A 'DORA TA A KANSA A TSAGA SHI GIDA BIYU, AMMA HAKAN BAI KANGE SHI DAGA ADDININSA BA. KUMA A TSEFE (comb) NAMAN JIKINSA DA MATAJIN QARFE A RABA (namansa) DA QASHI, AMMA FA HAKAN BAI KANGE SHI DAGA ADDININSA BA. NA RANTSE DA ALLAH, WANNAN AL'AMARI SAI YA CIKA, HAR SAI MAHAYI YAYI TAFIYA DAGA SAN'A'A ZUWA HADHARAL MAUTA (sunan gurare be) BA YA TSORON KOMAI SAI ALLAH, KO KUMA KERKECI AKAN DABBARSA, SAI DAI KU KUNA GAGGAWA NE "!
(Bukhari, hadisi mai lamba 3612).
KU QARA HAQURI !!!

Daga wakilanmu na Bauchi Zone.
Tare da (Ado Isah Guda).
08137925034

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post