CUTAR HAWAN JINI (Hypertension)


Chuta da magani

wato mukan ji hawan jini amman da munsan illarsa ga rayuwa dan adam da mun tausaya ma masu shi.
Hawan jini (hypertension) a takaice na nufin tsukewar magudanan jini wadanda kan haddasa ma zuciya wahalar harba jini zuwa sassan jiki.

Tabbasa hawan jini na da matsala matukar gaske.wanda idan ma mutum ya bar hawan jini a jikinsa ya dade be sha magani ba ko kuma be ma san dashi ba to yakan haddasa masa illoli da dama a sassan jiki,dan yakan taba zuciya,koda.ido
, harma da kwakawalwa.

hawan jini mace na iya kamuwa dashi haka namij,yaro haka babba,amman yafi kama masu yawn she karu daga arba,in abinda yai sama.
Yayin da mutum yasamu hawan jini zuciyar sa kan sha wahala wajen harba jini zuwa sassan jiki,wanda hakan kansa barin ta na hagu kan kumbura sbida ta nan ne jini kan fita.ko kuma yasa babbar jijiya me fitar da jini daga zuciya ta tsage, subanallahi!.
Idan jini ya hau yakansa bugawar zuciya ya karu wanda hakan ma yana iya kaita ga ta mutu kwatta kwata.ta rinka harba jini ba yanda ya dace ba, se jikin mutum ya canza,ya kamu da rashin lafiya.

ILLOLILINDA HAWAN JINI YAKE HAIFARWA.

1.yakan kashe zuciya kwata kwata, ko ya mata lahani
2.yakan shafi lafiyar idanu
3.yakan shafi kwakwalwa wanda kansa mutum faduwa,idan ya fadi ta hannunsa na dama to barin jikinsa na hagu zai mutu,idan kum ya fadi barin hannun hagu to barrin jikinsa na dama zai mutu.
4.yakan shafi koda da sauarnsu.
ABUBUWANDA KE HARDASA HAWAN JINI
Abu buwan dake haddasa shi
1.akwai yawan sinadarin cholesterol na cikin jini wanda yawansa kantoshe hanyoyin jini na zuciya hakan kan iya haddasa shi.
2. Akwai yawan tunani na bacin rai ko fargaba zasu iya haddasa shi.
3.sannan mutane masu yawan kitse ko kiba kan iya kamuwa dashi
4.sannan yawn shekaru ma na haddasa shi.

ALAMOMIN HAWAN JINI
1. Akwai juwa
2.karancin barci
3.ciwon kai
4.kaji zuciyarka na bugawa kamar ta zage fat fat fat sannan ga daya daga cikin alamomin juwa ko karan cin barci.

HANYOYIN KARIYA DAGA CUTAR WAHAN JINI
1. A rage yawan tunani na bacin rai.
2, Ga manya masu yawan shekaru, da masu kiba su rinka zuwa ana auna su.dan agane suna da shi ko babu.
3.yawan amfani da yayan itatuwa ko ganyaye.dan suka tema ka matuka. Wajen waraka da kariya daga cutar
4.yawn motsa jiki da rage shan gishiri.
Cutar hawn jini ana warkewa ta hanyar shan maganin da ke saukar da jini.

Daga: M.N.N UPDATES.
Tareda wakilinmu: Jibril Usman Sarki

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post