_cewar Abdulrazak sani
Masu Karatunmu Wannan Shi ne Kashi na uku A cikin Wannan Labarin dani Habib Rabi'u Nasarullah ke gabatar Muku Daga Shafin nan mai farin jini na MA'ASUMIYA NIGERIA NEWS UPDATES Asha karatu Lafiya.
Kamar yadda na kawowa masu karatun mu Bayan abdul da jawad sun fara magana ke nan malaman su suka shigo da supervisors domin raba musu jarrabawa zan dora daga nan inshaAllah.
Cikin wani irin yanayi me dauke da ban mamaki tare da sanyi jiki.
Na dubi jawad na ce zakzaky fa ka ce? Ya ce sosai kam dandanan na yi shiru na wasu da'ki'ka sannan na sun kuyar da kai na kasa ban yi la'akari ba sai naga (pen) nawa ya fadi, ya dube ni ya ce lafiya? Kafin ya rufe ba ki, sai na ji shigowar malaman mu domin su rabamana jarrabawa.
Jawad ya dube ni tare da dukan kafadata a hankali kamar sau uku sanan ya ce da ni cikin harshan turanci, ( Don't mind my friend later we are going to discuss inshaAllah)
Ya nufi gun zamansa ya zauna duk da ya ke sauran yan aji na ta faman surutu sukan malamai na ta ko karin sauran dalibai su yi shiru kamar yadda na hango wani malamin mu a lokacin me suna Kabir wanda kasan dalibai baka rabasu da sawa malami sunan banza.
Sunan kuwa yan ajin mu ke kiran sa da shi, shi ne ruwan (zafi).
Shakka babu bazan taba mantawa da wannan lokacin ba, wanda malamin nan duk zafin sa ya yi duk iya kar ko karisan akaina amman a banza wanda bansan iya kacin dukan da ya yiman ba. Na durkusa kasa na dauki birona. Sannan na nufi gun da jawad ya ke jikina a sanyaye na ce da shi idan ka kammala dan Allah ka jira ni, ya dube ni ya ce ok kar kadamu.
Hakika a wannan rana zan iya cewa jarrabawar nan ni dai na zana ta ne kurum domin na rasa menene ke yimin da di, musamman yadda zuciyata ta cika da wasi-wasi tare da ban al'ajabi domin ko a mafarki zuciyata bata taba sauwalamin zan ji jawad zai furta wannan kalami ba, duk da cewa shi ne dalibin da duk makarantar mu ka-kaf babu me kyawun dabi'ar sa da hakurin sa, da kawaicin sa da girmama na gaba dashi, shakka babu malaman mu suna mutukar alfahari da shi, bazan ta ba mantawa ba, duk wata gasa da ake sawa tsakanin makaranta da makaranta jawad shi ne ke daukar ta, da duk kan wata lambar girmamawa, duk da cewa mutum ne wanda ko irin soyayyar ajin nan da ake samun dalibai ke yi tsakanin maza da mata shi sam-sam ba za ka ce ga budurwar sa ba, duk da ya ke yan matan ajin mu sun sha nuna masa soyayyar da rubuta masa wasika amman shi ko tatasu ba yayi bazan manta ba mace daya ce ya taba rubuta mata wasika ya bata ya na me ba ta hakuri, musamman yadda ta kamu da san shi. Wanda karshe har sai da takai gata fadi a wannan lokacin malaman mu suka sami labari sukai abin da suka yi na daukar mataki wanda ko mu da muke yan iskan aji jawad ya na burgemu sosan gaske.
Da kammala za na jarrabawar sa ya mika ya fito. Ni kuwa daman zan iya cewa ba wani abu da nake da ya'kinin zan ci, fitar sa ke dawuya na bi bayan sa.
Har wani malami ya dube ni ya ce to malam abdul yau kai ne da carbi? Na yi murmushi na bashi na fito da fitowata idanuna basu kalli ko ina ba sai hange domin naga inda jawad ya ke, kamar ance da ni kalli can sai na hangoshi a wajan wata bishiya ya na tsaye sanye da glass na sa a fuska.
Na nufi gun sa gaba daya jikina a sanyaye, shima kamar ance da shi daga kan sa sai ya hangoni ya ce badai ka ce ka kammala ba? Na ce da shi na kammala sannan ya ce to Allah ya bamu sa'a na yi shiru domin amin ma ta kasa fita daga bakina sakamakon ni san zangon da na tafi a duniyar tuna ni da kuma abin da yafaru da ni jiya.
Jawad ya ce da ni abdul dazu na ji ka na tambayata akan wanene ya yi wannan karatun? Na ce da kai zakzaky ne ka cika da mamaki ban san menene ya ke faruwa ba? Na yi shiru san nan na nisa na ce e gaskiya dolane na yi mamaki. Domin gaskiyar maganar irin abubuwan da nake ji jama'a na fada musamman akan shi'a amman ni ina mamaki jawad kai kuwa a ina ka hadu da yan shi'a har kasami karatun malamin su? Ko kuwa kaima kazama dan shi'a?
Jawad ya dubeni ya yi murmushi ya ce da ni wai kai bakasan da cewa ni dan shi'a ba ne? A dai dai wannan lokacin sai na ji kamar jawad ya dabin wuka a kahon zuciyata ban ankara ba sai naji wani gumi ya karyomin da zafin sa kai kace wanda ake azabtar wa. Cikin ban mamaki na ce dashi yanxu kai dama dan shi'a ne? Duk da haka jawad ya ce tabbas abdul, batare da bata lokaci ba na ce shin yaushe kazama dan shi'a ya dubeni ya ce ai duk gidan mu su ne, na yi ajiyar zuciya dumin na farko ina tunanin irin cin mutumci da zagi da aibatawa da mu ke yi musu amman duk da cewa bamu da dabi'a me kyau amman muna zagi da aibatawa da jafa'i iri-iri akan su, ashe duk irin wanna abu da mukeyi muna shuka a idon makwarwa.
Jawad ya dubeni ya ce shi ilimi ba ruwan sa da a wajan wa yake ka amfana da shi ka yi aiki da shi, shi ne ba wai lallai sai ka na da wannan akidar ba, kaga ni ba malamin da bana saurara.
Abin ya dauremin kai domin yadda naji ana aibatawa da zagi da cin mutumcin su, ya na bani mamaki wanda ni a sauraran da na yi ni na karammu.
Hakika mun tattauna da jawad wanda na yi masa tambayoyi daban daban da ban kama tun daga kan zagin sahabbai, zagin matan annabi, da cewa wai basu yarda da annabi da sauran abubuwa da ban daban da muka tattauna
Danna Tsawan Rubutun na domin kashiga Shafinmu na Facebook:MA'ASUMIYA IN FACEBOOK
Wanda lokaci bazai bani ikon fayyace yadda muka yi da shi ba,Da farko jawad ya nunamin cewar dole kazamo me neman ilimi na addinan domin shi ne zai ban bace maka gaskiya da karya hakika ya kwadaitar da ni sosan gaske wanda bayanan da yayimin na sami nutsuwa sosai-sosai.
Musamman alokacin da nake tambayar sa menene shi'i?
Budar bakin sa ya ce dani yadda da imaman cin imam Ali da yayan sa, sannan sai aiki me kyau bayan imani da Allah da manzan sa.
Wanda akarkashin wannan mun yi magana me tsayi daganan muka dawo fannin zagin sahabbai budar bakin sa ya ce dani ku kawomana kalar zagin da muke yimusu? Wanda kai na ya daure amman duk da haka zuciyata bata gamsu da duk abin ya fadaba.
Hakan yasa na dauki damarar bincike a wurin maluma daban daban.
Wanda na dauki tsawan lokaci xuciyata ta na cikin damuwa bayan kammalawar mu ya ce ni fa ka gane ba nace ka yi shi'a ba a'a mu kullum abin da sayyid ke horar damu mu dage da bautar Allah da gujewa sabon Allah da yawan salloli sabo da haka burina abdul kazamo nagari da ya ke akwai inda zamuje ni da abban mu yau naga ga drivern gidan mu nan tahowa amman inshaAllah zamuyi waya ni dai bance da shi kalaba sai can xuwa jimawa na ce ok ba matsala.
Muka gaisa sannan ya shiga motar gidan su driver ya jashi ya tafi haka ya barni cikin tunani amman duk da haka zuciyata tana cike da tsoran lahira musamman abubuwan da naji jiya da daddare.
Haka ni dai na yini tamkar mara lfy.
Zan ciga ba dan a ji yadda zata kasan ce daga dan uwan ku
Habib Rabiu Nasrallah Tare da Daukar Nauyin Shafin nan Na MA'ASUMIYA M.N.N.U
_______________________
Yanzu fa labari yake domin Bamusan wani Hali Abdol zai komaba?
Sannan ya zatakaya tsakanin Abdol da mahaifansa??
Yaya Zai Zama Dan Shi'a bayan Wasi-wasi yana cin karo da zuciyar shi,
Mi kuma jawad zaice dashi a gaba????
Mu hadu kashi Na hudu A wannan Shafi Mai Albarka.
_________________________
Editing Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999
Tags:
Labari Na