'YAN MU'ASSASA BASA JITUWA DA MUTANE KO KUMA ACE SUNCIKA JIJJI DAKAI

_Inji Abdulhay A Ridwan_

Wannan Firar da Shafin Ma'asumiya Nigeria News yayi da Fitaccen mawakinnan daga cikin Wulayatul Haq a kwanakkin baya acikin Shirin FILIN MAWAKA Asha Karatu Lafiya.
〰〰〰〰〰〰〰〰〰
Ma'asumiya::: Dafarko masu karatunmu zasuso ka gabatar musu da Kanka??

Na'am. Sunana Abdulhay A. Ridwan. An haifenine acikin garin zaria kaduna state. Cikin wata anguwa wadda ake cewa kwarbai. Makarantar da mahaifina yafara sani shine Makarantar Fudiyyah wadda akayita a kwarbai kafin waqe'ar gwamnatin Abacha. Kasantuwar waki'ar Abacha ya da katar da karatuna. saida nadau tsawokaci sannan akasani Makarantar gwamnati daga bayan nayi nisa, sai mahaifina yamaida ni sabuwar Fudiyyah da aka bude abirnin zaria. Ina daga cikin daliban farko da aka yaye a wannan Makarantar, Na kasance bani da wasu abokai da suka wuce abokan da mokai makaranta dasu. Hakan kuma yasamu ne sakamakon Ra'ayin da ni nakedashi ina Abota dakaine idan ya zamana Manufarka Allah, Nifina kai addini kasa agaba. Wannan yasa har nagirma banda wasu abokan azo agani. Ni mawakine ayanzu sannan kuma Actor ne afagen film da sauransu
Hakan yasa yazam duk abokan da suke tare da ni abokan akine, Wani Irin aiki? Aikin da yashafi cigaban Addini musamman ma taimakawa da awar da (SAYYED ZAKZAKY H) yakeyi domin a irin nawa tunanin In bakada ra'ayin taimakon addinin Allah to kai ba abokin tafiya bane,

Ashekara ta 2015 waqe'ar gyallesu aka kashe manyan abokan da kwana ke rabani dasu wanan yamun ciwo sosan gaske tayanda bazan taba mantawa da cutarwar da gwamnatin Nigeria taimunba.

Kaman yanda nace da farko sunana Abdulhay amma anfi sanina da Smart Abdul sabida shine nafi anfani da shi a yanar gizo ko waqe da sauransu
Wanan shine ataqaice,

Ma'asumiyya: kakasance daban a cikin sauran mawaqa
Bisa irin salon da kake gabatar da waqokinka sakamakon sauran mawakan miyaja hankalinka akan haka???

Smart::Hakane kasan kowani dan adam dakagani zakaga yana da wani keban tacciyar ra'ayi tasa wanda yake da ita, saidai inyazana shi bame tsanan tawabane akan ra ayinsa sai kaga suna musharaka da wasu acikin ra'ayoyinsa na tsarin tafi da rayuwarsa.

Ma'asumiya : Wulayatul Haq da Mu'assasar Abul fadal abu dayane ko kowanne yana zaman kansane???

KARANTA WASU LABARAN ANAN:Bakusan Cewa Wayar Android Na dauke da Abubuwa Goma wadanda Takeyi ba?

Smart::"Na'am Wilayatulhaq wani sashine daga cikin sassan harka Mu'assasatu Abul fadl, so ita kuma Wilayatulhaq bangarene da ya shafi media na cikin Mu'assasa.

Ma'asumiya ::Wasu suna kallon ita kanta Mu'assasa a matsayin wata aba mai wani tsari da yabambanta dana harka, ku a wajenku ya abun yake domin kawar wa al'umma wannan matsala??

Smart::"Na'am kasan masu magana suna cewa dan Adam makiyin abun da yajahiltane. Da dama amun irin tambayan nan abaya kaman ace yan mu assasa basa jituwa da mutane ko kuma ace suncika jiji dakai kokuma wani dai abu daban. Yawacin mutane suna gina saninsu da Mu'assasa ne akan abunda sukaji wasu nafada, wannan yakasance maqiyine ko kuma sabanin haka. Kaman yanda yazamana mutanen gari suna samun Labarin da'awar sayyed ne yawanci ta hanyar makiyan SAYYED H din sai karshe insuka gana da SAYYED H sai su fahinci ashe sharri kawai ake masa. Wannan shine abunda yake faruwa da Mu'assasa. Dayawan wadan da sukai mu'amala da Mu'assasa karshe suna iya fahintar cewa daman asalan makircin maqiyane kawai Nasan sukawo farraqa cikin da awar SAYYED H shiyasa ake fakewa da sukan wasu bangarori da kuma sa shi da suke taimakawa da awar shi jagoran. Shi aiki shine ke nuna Asalin kalan mutun nahaqiqa. Da aikin kane ake gane meye ma nufanka da hanquronka,
 Kuma na tabbata babu wani me hankalin da zaikalli Aikin da Mu'assasa keyi yaji bayada sha awar yai taraiya dasu waje mu amala. So ni abun da zance gaduk wani me mummunan kallo ga yan Abul Fadl shine da yai makansa kiyamullaili ya daina sabida kallan mumini da mummunan kallo yasaba wa tarbiyar Addinin Musulunci.

 Sannan kuma kaman yanda yazo a qissa Allah s.w.t yana cewa, MUMINAI YAN UWAN JUNANE TO KUSASANTA TSAKANKANIN YAN UWANKU. To haka yake in baka zama me nuna so da kauna tsakani da Allah ga dan uwanka na addini ba to karka batashi gurin wani don kai bakasan shiba.


Ma'asumiya :: Tun farkon mu'assasa ta faro ne da Wilayatulhaq
ko kuma sai daga baya ta bayyana???
Smart ::Tunfarkon ta farone da Wilayatulhasq saidai mutanene basu saniba.
Ma'asumiya :::To amma ya tsarin wakokin suke a wajenku????

Smart::Kowane mawaki ko kuma ince mawaka zakaga suna da wanda suke kwaikwaya a wakensu. Misali matasa yanzu zakaga hangensu shine turawan yamma da sauransu. Kuma wannan a gaskiyar Al'amari su turawan yamma lalata Addini sukeyi dan daman su makiya Musulunci ne.
So mukuma mawakan mu na Wilayatulhaq kaman yanda aka Sanmu akai shine yakar duk wani abunda yake san yagusan da hasken Addini ta janibin wakoki da makamantansu.

 Wannan shiyasa kaga wakokin mu sunfita da ban da na saura sabida muna tafiyane akan Hadafi.
ko wane mawaki dan uwa yana iya shiga ko ankebe ne ga wasu kididdigaggun mutane?

Wilayatulhaq ma aikatansu akebe suke amma kowani mawaki zai iya aiki dasu in zai iya bin tsarin da suke. Sabida hakama yasa akwai wasu groups din mawaka da suka hada da (Anti bad boys, sky boys da Ahlul kisa'e) da suke tafiya taredasu bisa tsarin da ya dace.

Ma'asumiya :::Wacce hanya mutum zaibi idan yanason bada gudummawarsa a wannan tsarin?

Smart:::"E muna daukan ma aikatan da suka nuna sunasan tafiya damu lokaci bayan lokaci.
 Game san bada gudun muwansa zai iya tuntubar wakilan su ko cikin mawakansu sai yai masa bayanin yan da tsarin yake.

Ma'asumiya ::kanayin waka wani lokacin a kashin kanka??

Sosai ma kuwa
Ina waka na kashin kaina amma itama bata sauka da ga kan turbar da Wilayatulhaq ke tafiya akai

Ma'asumiya ::Zuwa yanzu wawoqinka sunkai nawa?
Gaskiya bazan iya sanin yawan waqoqinaba

Ma'asumiya ::shinko kana da bankadamiya Acikinsu??

Smart:::Akwai wakar da nayi me suna (Alkawari 2) wannan wakar ta kasance wanda nafiso acikin wokokina sabuda tana tunatar dani Abubuwa da daman gaske

Ma'asumiya ::To ko za a dan rero ma Masu karatun mu kadan daga ciki??

Smart:: MUNYI BARA A, YA SHUHADA MUNA JINJINA JININ DA KUKABA SHUGABA.

Munmika bai ar mutuwa ga zakzaky Abadan bazamu juyaba.

Daa karun Abulfdl zakzaky shi mukkadauka shugaba.

Zamu bada rai jini da lokaci dan islam yaja gaba.

Lallai mumun dau Alkawari bazamujada bayaba.

Alkawarin damukawa rabbana yan uwanmu su suncika,

Sauramu lokaci yana zuwa shahada garemu daukaka,

Munburin muzamto Akarbala mubadarai kare mai maka,

Alhmdullh awanga zamani jininmu dominsa zai zuba

Ma'asumiya :: Shukran nima nadau Charji (Murmushi) Ko Akwai wasu tsare tsaren da kuke dasu Don bunkasa wannan lamari kangaba??

Smart ::"E muna da burin ya zamana duk wani matashi ko kuma duk wani wanda yake da daman taimakawa ga addini, ya tashi tsaye wajen bada gudun muwansa. Mu agurin mu in wannan yasamu zai zama sakon SAYYED H zai yadu ko ina (kowa yatashi yai aikin da yahaukansa) wannan shine

Ma'asumiya:::Zuwa yanzu wacce nasara kuka cimma?
Smart ::Na am Alhmdullh matasa dadama suna fahintar sakon da muke tura musu ta wake ko ta sura(poster) kuma insha Allah muna saran nan gaba kowama ya dunga fahintar sakonnin mu ciki da waje manya da yara.
Ma'asumiya ::Shin akwai kalubale da kuka fiskanta,ko kuke fiskanta?

Smart::E to bazamuce bamu fuskantar wata matsalaba tunda kasan zaman yau da kulun, Kowa yasan yanayin kasan da muke ciki a Nigeria ana fama da rashi, Wannan yakan dan dakatar da mu wajen gudanar da wasu Abubuwan da mukasa agaba wani lokaci.

Ma'asumiya ::Minene kiranka ga Gwmanati, Al'umma da kuma 'yan uwa kan zaluncin da akayiwa jagoran wannan harka?

Smart:: Ita dai waqe'a dolene arayuwar muminai, so in tazo dolene sui hakuri,
Amma gadukkan mumini dolene yaita kansa daga cikin rayuwar bautar war Azzalumai dakuma zama cikin kaskanci. Kira na ga yan uwa ma'abota Harka Islami shine su dage, sujajirce, sukuma cije akan kiran da SAYYED ZAKZAKY H yakeyi, Wato Bujirewa dukkan wani Azzalumi da kuma zalunci tare da mika wuya ga Tsantsar Addinin gidan manzon Allah s.a.w.w,
Da aiki da koyarwarsu dakuma Al qur'ani. Domin Nigeria ba a anfani da dokan Al'Qur'ani sai dokan makiaya Al qur'ani.
Matasa sune kashin bayan Al umma, so matasa ayanzu zama be ganmuba. Domin inkace zaka nemi duniyane awannan lokacin bazaka sametaba me zai hana kanema lahiran ka da lokacin ka da jininka gobe kiyama kaje gurin Allah kana cikin wayanda ake wa bushara da Aljanna. Lallai yakamata mutashi mutaimaki SAYYED ZAKZAKY H.
Gwamnatin Nigeria Jahilar gwamnatine wadda batasan inda tadosaba. Sukansu masu Mulkin inda zaka tsare su katambaye su mene suke anfana dashi acikin irin Mulkin dasukeyi. Zakaga kame kame kawai suke sabida basu da wani hadafi illah Shirme da shiririta,

So yunkurin gwamnati naganin ta dushe Hasken Allah adoran qasa wowtane kuma bazai daureba. Wannan shine mafarin rushewanta. Kuma wanan shine karshen duk wani me fada da Addinin Allah.

Ma'asumiya ::Muna godiya
Smart: Nima ina Godiya

Rubutawa : Salisu Umar mazaje

Editing Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post