ANAN WURINSU ZAMU DAWWAMA HAR MU MUTU BAZASU KAIMU ASIBITI BA!!!



Tun bayan Waki'an Zariya nake jinyan Kafa na har yazuwa yanzu...
- Inji Zainabul Khoubra a firar da Wakilinmu yayi da Ita ta wayar Salula ga Yadda Firar takasance Asha karatu lafiya

Ma'asumiya;  MASU KARATU ZASU ZO SUJI SUNANKI?

Radiya: Sunana Zainabul Khoubra Muhammad (Radiya).

Ma'asumiya: KINA DAYA DAGA CIKIN WADANDA SOJOJI SUKA DIRARWA A ZARIYA KO YA WANNAN AL'AMARI YA RUTSA DAKE?

Radiya: To, insha Allahu da yake dai abubuwan da yawa, amma dai a takaice dai daman an sani ranar saka tuta ne to sai ya zamo mun shirya zamu wuce saka tuta din a Zariya sai muka ji sojoji sun zagaye Hussainiyya sun fara harbi. To da yake zamu tafi ne a daidaiku sai aka ce ya kamata mu tafi a tare a mota guda sai muka tafi, a lokacin da muka kama hanya sai muka yi waya da wani a Hussainiyyan yake ce mana sai dai Mu wuce Gyellesu amma Hussainiyyah babu hanya zuwa. Sai muka wuce Gyellesu muka sauka muna ta Addu'oi har dai Magriba babu wani labari cewa sun zo nan Gyellesu din.

To da har mun 'deciding' cewa ko zamu dawo gida ne ma sai Ameer namu na Garin Soba wato 'wakilin 'yan uwa na garin mu' yace babu bukatan dawowarmu mu zauna. A wannan lokacin har mun fara bacci haka sai muka ji wani kara sai aka ce to ai gashi ma har sun zo kusan karfe Goma da Rabi 10:30Pm to sai suka fara harbi a wurin kofar 'Banadin' ana dauko majinyata nan dai aka kwana anayi dai, suna harbi sosai sosai.

Ma'asumiya: YA KIKAJI DAI-DAI LOKACIN DA SOJOJI SUKA FARA HARBIN KU ?

Radiya; A da yake dai al'amarin waki'a dole mutum zai ji wani abu a ranshi, duk da dai ba shi bane waki'a na farko da na fara gani ba to amma gaskiya na girgiza ba laifi musamman ma da naga sojojin basu jima da zuwa ba suna ta harbi ana ta dauko marasa lafiya wasu kuma sun zama shahidai ma, gaskiya naji ba dadi a wannan wajen.

Ma'asumiya; DA SOJOJIN SUKA ZO SHIN SUNYI MAGANA NE KO KUMA HARBI KAWAI SUKA FARA ?

Radiya; Gaskiya basuyi magana ba suna zuwa kawai suka fara harbi duk da cewa akwai wani mai shayi a wurin kawai sai muka ga wajen ya kama da wuta mu bamusan me sojojin suka sanya ba kawai munga wuta na ci ne. Ranar Lahadi bayan sun zo sunyi kisan su sun zo wajen gidan Abba to mu muna kofar gidan Abba din to sai ya zamo harbin Sojojin yayi yawa sai muka bar wurin a wajen aka harbi wata sister sai muka dauke ta muka kai ta gidan Harisawa.

KARANTA WASU LABARAN MU:Na rubuta tambayoyi 25 da Zanyiwa Sheihk Ibraheem Zakzaky (h)

To bayan an shiga da ita gidan Harisawa kafin mu fito su kuma sojojin sun iso kofar fito wa din, nan take suka fara harbi anan din daga baya sai muka ji zafin wuta sai aka ce mu fito daga gidan da muke ciki sai suka fara harbin mu suna cewa muyi saranda kokuma duka su harbe mu, to sai Malam Mustapha Lawan Nasidi Potiskum yace babu bukatan a musu saranda to shikke sai suka cigaba da harbi to ni ma dai anan ne aka harbe ni sai suka kama wanda zasu kama suka tafi dasu.

Ma'asumiya; TO DA SUKA HARBEKU YA SUKAYI DA KU HAR KUKA KUBUTA DAGA HANNUN SU KUNA MASU RAUNI A JIKI ?
Radiya; Bayan sun harbe mu sai suka sama gidan wuta, to akwai wadanda suke dan iya mike wa haka sai suka tafi dasu mukuma sai suka bar mu. Bayan sun tafi sun barmu nan dai muka kwana cikin gidan na Harisawa nan da safe sai suka sake zuwa ranar Litinin da safe kenan suka zo suna dubawa ko akwai wanda basu mutu ba a cikin mu da suka duba sai suna buga musu wukan bakin bindigan su suna karasa majinyatan, suka kwashi gawawwakin kuma suka tafi dasu. A ranar litinin din da yamma sai suka kara dawowa to abinda muke tunani a lokacin ne suka fita da Abba (Sayyid Zakzaky H) da yake mu muna gidan Harisawa ne ba zamu ce a wani lokaci suka fita dasu Sayyid ba amma muna Kyautata zaton a wannan lokacin ne da suka kara dawowa da yamma. Bayan kuma anyi Magrib lokacin karfe shida ta wuce sai suka kara dawowa suna kwashe gawawwaki nan suka tarar damu da sauran rayukan mu a gaba muma suka di bemu suka tafi damu 'Deport' din su na Sabon Gari.

Ma'asumiya; BAYAN SUN KAI KU DEPOT DIN SOJOJIN SUN KIRA A ZO A KWASHE KU NE?
Radiya; A'a dama tun lokacin da suka kai mu ranar litinin din kenan da daddare sai suka ce anan wurin su din zamu dauwama har mu Mutu ba zasu kai mu asibiti ba to daga baya sai wani Kirista yazo yace musu ya kamata su di bemu akai Mu asibiti saboda jinin mu yana zuba sai suka daure mana washe gari talata sai suka kai mu asibiti. A ranar Talatan da misalin karfe Biyar 05:00pm haka na yamma suka kai mu asibiti 'Shika'. A ranar lahadi sun kai wasu 'yan uwa asibiti haka sai ya zamo mu lokacin da aka kai mu 'Already' akwai wasu 'yan uwa majinyata haka a asibitin. Sun kai mu sai suka yi magana da su likitocin asibitin cewa idan akwai wasu daga cikin mu suka mutu to a sanar dasu kada a bawa kowa gawan. To a nan wani likita yace musu wannan kuma ba aikin ku bane na su ne, tun da su dai sun riga da sun kawo shikke nan. To bayan sun tafi sai 'yan uwa suka zo suka cigaba da bamu kulawa.

Ma'asumiya; TO YA JINYAN KI YA KASANCE BAYAN WAKI'AN ZUWA YANZU ?
Radiya; Har izuwa yanzu haka ina jinya da sauran karaya da na samu a cinyata har yanzu dai ina jinyan wurin.

Ma'asumiya; TO WANE SAKO ZAKI BAYAR KO KUMA WANI KIRA ZAKIYI GA SU SOJOJIN DA SUKA YI WANNAN AIKA-AIKA NA TA'ADDAMCI AKAN ALMAJIRAN SHEIKH ZAKZAKY.?

Radiya; Kirana ga ita wannan Gwamnati shine su sani cewa mu kamar yadda jagoranmu ya saba fada mu barazana da kisa bata karamana komai sai dakewa, kuma wannan abin da suka mana sun mana ne domin mu tsorata muce mun bari to mu wallahi wannan ya tabbatar mana da cewa muna kan hanya kuma daman mun riga mun sani haka hanyar take suma zuriyar Manzon Allah (S) haka ya faru dasu. To muma bama bakin ciki da abinda suka mana bilhasani ma farin ciki muke kuma muna rokon Allah ya tabbatar damu yasanya karshen mu ya zama shahada kamar yanda 'yan uwan mu suka yi kisan da suke yi ba zamu ce su fasa ba domin shine gadon gidan su muma kuma ba zamu fasa ba kuma gwagwarmaya yanzu ma muka fara kuma sai ya tabbata a Nigeriya ko sun ki ko sun so.

Ma'asumiya; SU KUMA 'YAN UWA MASU KARATU WANI SAKO KIKE DASHI DA ZAKI FADA MUSU ?
Radiya; Yana da kyau ga 'yan uwa a kara dagewa mu kara jajircewa abinda na sani suma Ahlulbait sun yi fama da irin wannan abubuwa din. Jajircewan mu da dakewanmu shine zai sa Allah ya dube mu ya bamu babban rabo, 'yan uwa ya kamata a jajirce musamman a halin da muke ciki ya kamata mu jajirce har Allah ya kwato mana jagoran mu Sheikh Zakzaky (H)
Ma'asumiya; AMMA YA KIKE JIN YADDA AKE ABUJA STRUGGLE GASHI KINA FAMA DA JINYA MAI TSANANI.
Radiya; To insha Allah nima ina burin na kasance cikin masu Struggle na Abuja.

Wannan tattaunawa ne da Idishia Jos wakilin Ma'asumiya Nigerian News Update yayi da wata baiwar Allah a Garin Soba na jihar Kaduna Nigeria mai suna Zainabul Khoubra Muhammad (Radiya) akan ta'addancin da sojoji suka yi a gidan Malam Zakzaky (H) dake Unguwan Gyellesu nan Zariya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post