Waqa
Part 2
Lallai Sayyid Zakzakyyu ne hasken zamani,
Kubimu cikin nutstsuwa kusan shi kusan Addini,
Tun kafin haifarsa an fade shi a manyan Karni,
Manyan bayin Rabbi sun fadeshi domin mussani,
Busharori sun fito a kansa hasken Addini,
Sharfuddeeni lakkabinsa ma daukaka Addini,
Imam Aliy yayo batunsa domin mussani,
Imam Jafar as sadik Dan fodio sun yo tuni,
Dk sunyi batun sa a zahiri harma badini,
Shi Imam Jafar ga batunsa dan daure kassani,
Busharatul Islamu nemo don kassani,
Cikin zancen Mahady mai gyaran Addini,
Da sunayen jarumansa masu cikar Imani,
Guda dari uku da sha uku wannan zamani
Sune gwarzaye mataimakansa akan Addini,
Dukkansu tsayayyune jarumai a cikin Zamani,
Yace a cikinsu akwai Ibrahimu hasken Addini,
Da zaya fito daga magarib tabbas mun gani,
Waliyai ne dukkaninsu masu cikar Imani,
Sune Takuban rabbana da zasuyyi Gwagwarmaya.
_________________________
Amshi= IMAM TAKA LAFIYA AL'ZAKZAKY IBRAHIMU SADAUKI KAKE KI GUDU MAI SANYA MAZAJE GUDU
______________________
Daga
Ma'asumiyya Nigerian News Update (M.N.NU)
Tare da
Salisu Umar Mazajen Zakzakyya
08021395846
Tags:
Labari Na