TSOKACI KAN YADDA AKE HADA WEBSITE


_Kashi na biyu

_____________________________
Daga shafin Ma'asumiya Nigeria news updates
_____________________________
Mun tsaya ne inda muke cewa; Gaba daya website ko kuma shafin internet za’a iya raba shi gida biyu ta la’akari da yanda ake hada shi (wato web design ) da kuma abubuwan da ake amfani da su wajen hada shi. Hada website ko kuma web design ya kasu zuwa gida biyu kamar haka:
1. Sashen da ake iya gani idan an ziyarci website din (wato Front-end )
2. Sashen da mutum wanda ya ziyarci website din baya iya gani (wato Back-end )

1. SASHEN DA AKE GANI IDAN AN ZIYARCI WEBSITE(FRONT-END)

Shi front-end, ko kuma sashen da ake gani idan an ziyarci website, ya kunshi duk wani dubaru da ake iya amfani da su wajen yin designing ko kuma tsara duk wani abu da ke a cikin website wanda idan mutum ya shiga website din zaya iya gani. Abubuwan da za’a iya gani a cikin website sun hada da hotuna, videos, rubutu, audio da dai sauransu. Ana amfani da abubuwa biyu zuwa uku ne wajen designing din front-end na website.

Na daya, kuma jagora daga cikin wadannan abubwa da ake hada website da su, shine HTML (Hypertext Markup Language). Shi HTML yare ne na computer (ko kuma programming language) wanda kuma shine ginshiki na ko wane irin website da ka sani, domin da shi ne ake designing din taswira, tsari ko kuma skeletal na website. Da HTML ake amfani wajen sanya rubutu, hoto, video, malatsai (buttons), wajen da mutum zaya iya sanya rubutu (wato textbox) da dai sauransu. Duk wani abu da ka sani zaka iya tabawa ko kuma aiwatar da wani abu a cikin website ta hanyar shi wannan abun, to ana amfani da HTML ne wajen sanya shi.
Baya ga HTML, abu na biyu da ake amfani da shi wajen yin design din front-end (wato sashen da mutum ke iya gani) na website shine CSS (Cascading Style Sheet). Shi CSS ana amfani da shi ne a website domin kayata website din ta hanyar sanya wasu abubuwa kamar su kaloli (colors), zane da kuma positioning (wato kuma tabbatar da cewa duk wani abu da aka sanya ta hanyar HTML to an dora shi a inda ya kamata). Ba don CSS ba, to da website bai yi kyawon da muke ganin shi da shi ba a yau, domin idan ba’a yi amfani da CSS ba wajen designing din website, to kusan komi da ke cikin wannan website zaya fito ne cikin layi guda ko kuma duk su hade a waje guda ta yanda ba zaka iya rarrabewa a tsakaninsu ba.
Daga CSS kuma, abu na uku da ake amfani da shi wajen yin designing na front-end (wato sashen website wanda mutane kan iya gani) shine
JavaScript.

KARANTA WASU LABARAI ANAN:ISAH ALMASIHU ZAI DAWO DOMIN YIN WASU AYYUKKA BIYU

JavaScript shima yaren computer ne (programming language) da ake amfani da shi wajen sanya website ya zama dynamic, wato website mai sauya kamannu kuma wanda ke iya amsa bukatar mutum (misali wajen yi rajista ko kuma Log in). Dynamic website shine website wanda mutum zaya iya neman wani bayani (ko kuma searching din wani bayani) kai tsaye a cikinshi kuma ya maido ma mutum da amsar wannnan bayani da ya nema. A lokaci guda kuma ta yanyar javascript, za’a iya sanya website din ya nemi ko kuma ya tambayi mutum wani bayani wanda za’a iya amfani da shi wannan bayani a cikin website din ko kuma wani abin daban. In aka so, Za’a iya design na website ba tare da javascript ba amma kuma yana da matukar amfani musamman ma idan mutum yana bukatar wannan website ya zama dynamic.
Wadannan abubuwa guda uku, wato HTML, CSS da kuma Javascript, sune ake amfani da su wajen designing ko kuma hada sashen website wanda mutane ke gani idan sun ziyarci website din (wato front-end). Mutum wanda ya san wadannan abubuwa guda ukku (HTML, CSS da Javascript) kuma yake hada website ta hanyar amfani da su, shi ake kira da
FRONT-END DEVELPER wato wanda ke designing na sashen website wanda mutane ke iya gani idan suka ziyarci wannan website din.

Zamuci gaba kudai Ku kasance da shafin Ma'asumiya matattarar ilimummuka.

Tare da Wakilinmu Mas'udu Dan masani Shinkafi 08149993999

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post