BANA SON BUHARI SABODA YANA KASHE YAN UWANSA MUSULMI!!

MA'ASUMIYA NIGERIA NEWS UPDATES

A satin dayawuce ne na shiga motar wani Igbo (inyamuri) a cikin motar sai naji mutane sunata hirar su ta duniya,akan matsalolin Nigeria musamman abinda ya shafe matsala rashin aiki stadar man fetur. Amman nidai bance komai ba, Amman abinda na fahinta duk masu magana hausawa ne.

Acikin maganasu naji wasu suna cewa mudai mukara hakuri baba buhari yana iya kokarinsa , wani kuma cewa yayi hmm haka zamu zauna munata hakuri yunwa tazo tana mana dauki day-day, hakadai naji mutane da dama suna fadan ra'ayinsu, Amman duk cikinsu suna goyon bayan buhari ne.

Mai motar da ya daukomu dai duk magana da akeyi baice komai ba, kuma yafahinchi nima banyi magana ba, sai ya kalleni yace halan niba Hausa bane? Nace masa ni bahaushe ne. Yace miyasa bakayi magana ba ? Nima nace masa miyasa kai bakayi magana ba? Sai yace aini inyamuri ne (Igbo) nace bakazabe buhari ba kenan? yace nayi zabe kuma buhari ne farkon Wanda na taba zaba kuma bazan Kara zaben kowaba.

Nadanyi dariya nace miyasa kaikuma bazaka Kara zaben kowaba?
Yace ni Igbo ne lokacin da Jonathan yana kan mulki nida kaina na bukachi yasauka saboda kisan mutane da akeyi, wannan ma yasa nayi katin zabe.

Amman bayan zabe sai naga bayan wahalar rayuwa da tsadar man fetur, haryanzu ba'adaina kashe mutane ba kuma abin takaici abin haushi kuma shine abinda yasa natsani buhari sabida yana kashe yan uwansa musulmi kuma ko ajikinsa, wanan dalilin ne yasa banason buhari kuma nace bazan Kara zaben kowaba.
Ra'ayin ibo kenan to kai kuma miye naka ra'ayin ???

Daga wakilinmu: Jibril Usman sarki, 08149953832.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post