"..Sojojin Nijeriya, Sun yiwa gidan mahaifina kawanya na wasu kwanaki, sannan suka far mishi, tare da yin amfani da muggan makamai don su share hanya, suka yi ta yiwa mata fyade da kisa yadda suka so. Haka suka kutsa da karfi har suka samu wani daki inda sauran mutane da suka rage ke ciki; a dakin ne iyaye na da ragowar kanne na uku suka samu mafaka.
A nan suka farma dakin da ruwan harsasai, har sai da suka tabbata cewa kowa baya motsi. Ina waya da Mahaifiyata, har zuwa lokacin da na ji wayar da ke hannunta ta fadi kasa, kuma na ji lokacin da Sojojin ke fadin
# this_one_no_die .’
sai kuma karar harsasai da suka ci gaba da harbawa. Dukkansu ina jin muryoyinsu a lokacin, suna kisa, amma ko a jikinsu…!"
-Sayyed Mohammed Ibraheem Zakzaky