FITINAR DA TA FI SHIRKA A BAYAN WAFATIN MANZO (S.A.W.W) !!!

Neman shugabanci/duniya shine babbar fitinar da Annabi (S.A.W.W) ya bari cikin al'ummarsa, ta kasance abu mafi girman hatsari fiye da shirka wajen tafiyar da imanin mutum.

Duk wanda ya kasance yayi imanin gaskiya ga Allah, to zai yi wuya ace ya juyawa addinin Allah baya. Amma in ya kasance me kwadayin shugabanci/duniya ne, abu ne me sauqi ya aikata abinda zai raba shi da imaninsa, alhali yana sallah, azumi da kuma aikin Hajji.

Wannan abu bai zame baqo ba, domin hakan ta faru cikin Sahabbai tun lokacin da Annabi (S) yabar cikinsu. Neman shugabanci shi yayi sanadin wasu shahadantar da 'yar Manzo (S.A.W.W), wasu kuma suka karkashe zuriyarsa.
To, ga shi wannan gubar da ta taso daga magabata tayi naso zuwa wannan zamani mai rudu da muke cikinsa. Malamai da sarakuna duk sun fada cikin wannan tarko me wuyar kubucewa.

KUYI LIKE DIN SHAFINMU NA FACEBOOK ANANMA'ASUMIYA FACEBOOK

Wannan fitina tayi sanadin rabuwar kai cikin addini, zumunci, tare da aikata duk wani nau'in na sabon Allah wanda zai yi sanadin tafiyar mutum zuwa wuta.

Za ku gaskatani matuqar kunyi nazarin yadda ake zubar da jinanan bayin Allah muminai ba bisa haqqi ba, sai dai kawai don neman rabbatuwa kan kujerar mulki wanda ba a tunanin mutuwa za ta iya raba su da ita.
Manzon Allah (S) ne ya bayyana mana haka cikin wani hadisi ingantacce wanda Bukhari ya riwaito shi kamar haka;
Sa'idu Bn Shurahbaili ya bamu labari, Laisi ya bamu labari daga Yazid, daga Abu Khairi, daga Uqbatu Bn Ameer cewa, wata rana Annabi (S.A.W.W) ya fito yayi sallah ga shahidan Uhud, sa'annan ya juya zuwa Mimbari yace;
" LALLE NI ZAN BARKU, KUMA ZAN YI SHAIDA A KANKU. WALLAHI YANZU HAKA INA KALLO ZUWA TAFKINA, KUMA NI AN BANI TASKAR MABUDAN QASSAI. WALLAHI BA NA TSORON KUYI SHIRKA A BAYANA, SAI DAI INA JIN TSORON ZA KUYI ( ta fadan neman shugabanci) A CIKINTA ".
(Bukhari, hadisi na 3596)

Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925034

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post