SHIN KINA/KANA FAMA DA AMOSANIN KAI ? GAWANI KARIN HASKE AKANSA

                     Chuta da magani

Daga shafin ma'asumiya Nigeria news updates.

Tareda :Jibril Usman Sarki (08149953832)

Babu kamshin gaskiya wai yana makanta ido. amosanin kai ba ciwo ba ne,
wato ba cuta ba ce wadda wata
kwayar cuta ke iya sa wa. Kamar
matsalar saba ta sauran fatar jiki da
wasu suke ganin kamar ciwo ne,
amosani shi ma saba ce da kan faru
a fatar kai wadda take karkashin
suma.

To idan tana barbashewa za a
ga fari-fari na zuba kamar gari,
musamman idan an zo taje kai ko
kitso ko an zo yi wa mutum aski.

Bari na danyi maka bayanin a kan ita
kanta fatar jiki tukuna, sa’annan ka
gane cewa ba matsalar da zaka
damu da ita ba ce sosai. Dama
fatarmu canzawa take daga lokaci
zuwa lokaci, kusan a ce wata-wata,
dangane da irin abinci da muke ci
da yanayin gari wato, zafi ko
hunturu ko rani ko damin, da irin
abin da muke shafa mata da kuma
yawan shekaru, wato tsufa ko
kuruciya. Duka fatar kowa tana son
abinci mai lafiya isasshe, mai dauke
da sinadarin abinci mai gina jiki
wato protein, wanda daga shi ne
fatar kan sarrafa sinadaran keratin
da collagen da elastin, wadanda su
ne ginshikan ita kanta fatar. Sai
kayan marmari masu dauke da
bitaman masu sa fata sheki da
walwala.

Sbd shi ba ciwo bane saba ce ta fata sannan kusan rabin duniya kowa na fama dashi,mata da maza sannan yana da kai kayi da zafi haka.
Sbd haka tunda ba cuta bace bashi da magani sai dai maganin da zai lafa ta kamun fatar ta kara yin wata sabar.

Akwai wani magani mesuna (Head and shoulder) ina ga kamar  yafi kowanne kyau kuma ana samunsa a ko ina.masu matsalar kan iya amfani dashi su rinka wanke kai dashi.amman shima ba maganinsa bane yana dai rageshi.

   Allah yasa mudace

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post