SAYYIDAH FATIMA (S.A) A HARSHEN MANZO (S.A.W.W) .



Sayyidah Fatima (S.A) tana da wani matsayi a wajen Allah (T) Wanda ba kowa ne ke da irinsa ba sai dai mahaifintav Manzo (S.A.W.W). Saboda haka ta zamo ta dabam cikin al'ummar Annabi (S.A.W.W).

Imam Ahmad yace, baban Sa'id baran gidan Banu Hashim ya bani labari, Abdullahi Bn Ja'afar ya bani labari, mahaifiyar Bakri 'yar Maswara Bn Makramata ta bamu labari, daga Ubaidullahi Bn Abiy Rafi'i, daga Maswara, shine Ibn Makramata yace, Manzon Allah (S.A.W.W) yace;
" FATIMAH TSOKA CE DAGA GARE NI, YANA FUSATANI ABINDA KE FUSATATA, YANA FARANTA MIN RAI ABINDA YA FARANTA MATA. LALLE WATA NASABA (ta mutum) TANA YANKEWA RANAR ALQIYAMA, SAI DAI NASABATA DA TAFARKINA DA SURUKUTATA ".
(Musnad Ahmad, J:4, Sh:323).

A riwayar da tazo cikin Bukhari da Muslim kuma, daga Maswara Bn Makramata yace, Manzon Allah (S.A.W.W) yace;
" FADIMATU TSOKA CE DAGA GARE NI, YANA FARANTA MIN RAI ABINDA YA FARANTA MATA, KUMA YANA CUTAR DANI ABINDA YA CUTAR DA ITA ".
- Bukhari, J:5, Sh:28.
- Muslim, J:7, Sh:140.
===== NAZARI =====
_______________________________
Idan akace nasabar Manzon Allah (S.A.W.W) da surukutansa ne kawai ba ta yankewa, anan ana nufin nasabarsa tsarkakekkiya neman da kuma Ahlul-Bait (A.S), domin nan ne surukutansa take wacce ta wanzu.
Kun san ance ya aurawa wasu 'ya'yansa, amma dai ba su da tushe wanzajje a tarihi.
To, ka da ku manta da wani abu kuma, duk wanda ya cutar da Manzon Allah (S.A.W.W) (directly or indirect), to Allah ya cutar.
Menene kuma matsayin wanda ya cutar da Allah?

Daga wakilanmu na Bauchi Zone.
Tare da (Ado Isah Guda).
08137825034

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post