RABON GADO (INHERITANCE) A MUSLIMCI (1)

Ka danna photon nan domin karantawa kati Shere domin wasu su affana.


SHIMFIDA
Shi rabon Gado a muslumci umarni ne na Allah da ya tsara shi cikin Qur'ani Wanda aka ambata a aya ta 11-12 da kuma aya ta 176 cikin Suratun-Nisa'i.
Saboda haka wajibi ne a yi shi matuqar sharuddansa sun tabbata, wato samuwar mamaci, magada da kuma abinda za a gada.
Inda ace biyu daga ciki za su samu, amma a rasa na ukun, to, da gado ba zai yiwu ba. Misali, ace mutum ya rasu ya bar magada amma babu abinda za a Gada, anan wanne rabo za ayi?
Shi wannan kaso ya zo cikin Qur'ani ne da sigar qasaru (fraction), kuma lamba shida 6 ne kamar haka:-
1/2, 1/4, 1/8, 1/3, 2/3 da 1/6.
== KASO DA MA SU CIN KASON ==
___________________________________
(1)- 1/2, Rabi shine kason Miji, 'ya, 'yar 'Da, 'yar'uwa shaqiqiya da kuma li'abiya bisa wasu sharudda.
(2)- 1/4, kwata shine kason mata 1 ko sama da haka, da kuma Miji bisa wasu sharudda.
(3)- 1/8, 'Daya bisa takwas kason mace/mata ne shi ma bisa wasu sharudda.
(4)- 1/3, 'Daya bisa uku kaso ne na Uwa idan 'Danta ko 'yarta suka rasu ba su bar 'Da ko 'ya ba.
(5)- 2/3, Biyu bisa uku shine kaso na 'ya'ya mata biyu ko fiye da haka, da kuma 'ya'ya mata na danka (son).
(6)- 1/6, 'Daya visa shida kaso ne na Uba da Uwa, wato kowannensu zai dau 1/6 daga cikin abinda 'ya'yansu suka bari, matuqar su ma suna da 'ya'ya.
Za mu cigaba insha Allah.
Daga wakilanmu na Bauchi Zone.
Tare da (Ado Isah Guda).
08137925034

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post