ANFARA SHARI'AR KISAN DAN JARIDA KAMAL KASHOOGI ______________________



ⓂKafar yada labaran Saudiyya ta rawaito an fara shari'a kan kisan dan jaridar kasar Jamal Khashoggi da aka hallaka a karamin ofishin diflomasiyyar kasar da ke Turkiyya a bara.


__Rahotanni sun ce mutane 11 da ake zargi da hannu a kisan sun bayyana a wat kotu da ke birnin birnin kasar wato Riyadh.


__Masu shigar da kara dai sun bukaci kotu ta yankewa 5 daga cikin mutanen hukuncin kisa.


__A ranar 2 ga watan Okobar bara ne aka kashe dan jarida Khashoggi, a lokacin da ya je ofishin diflomasiyyar Saudiyya dan karbar takardun shaidar rabuwa da tsohuwr mtarsa wand hakn zai bashi damar auren wata mace 'yar asalin Turkiyya.


__Masu shigar da karar sun ce, wata hatsaniya ce ta hada shi da mutanen da ke masa tambayoyi da kuma suke kokarin rarrashinsa ya koma gida Saudiyya anan ne kuma aka kashe shi.


__Hukumomin Saudiyyar dai sun ki amincewa da bukatar shugaba Racep Tayyep Erdogan na Turkiyya, na tasa keyar mutane 18 da ake zargi da aikata kisan kasarta dan su fuskanci hukunci, ciki har da mutane 15 da akai zargin sun yo takakkiya zuwa birnin Santambul musamman dan aikata kisan.


__Ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Adel al-Jubeir ya yi watsi da bukatar inda ya nanata ba za su mika 'yan kasarsu ba.


__Kafar yada labaran Saudiyya ba ta yi cikakken bayani kan yadda zaman kotun ya gudana ba, baya g cewa wadnda ke zrgi da lauyoyinsu sun bayyana gaban kuliya.


__Sai dai kuma ana nuna shakku kan ko mutane 15 da hotunan bidiyo na CCTV a filin jirgin sama na birnin Santambul ya dauka, da kuma gwamnatin kasar ta bada sunayensu na daga cikin wadanda aka gurfanar gban shari'ar.


__Lauyoyin sun bukaci a ba su shaidun da ke da su da ba su isasshen lokcin yin nazari, dan haka ba a bayyana ranar da za a ci gaba da sauraren shari'ar ba.


___Kamfanin dillancin labaran kasar PA ya rawaito cewa ministan shari'ar kasar Shaikh Su'ood bin Abdullah Al Mo'jab bai amince da bukatar da gwamnatin Turkiyya ta shigr na sanin shaidun da suke da su a kan kisan Khashoggi ba.


__Tun da fari wata sanarwa da ma'aikatar shari'ar Saudiyya ta fitar, ta sanar da karin mutane 10 da ake gudnar da bincike akan su duk dai kan zargin hannu a kisan.


__Tun bayan kisan dan jaridar ake nuna yatsa kan yarima mai jiran gado Muhammad bin Salma, wadanda Turkiyya ke so a mika mata sun hada da Saud al-Qahtani da Ahmad al-Asiri manyan na hannun damar yariman da kuma aka sallama daga bakin aiki bayan aikata kisan.

___________________

Ma'asumiya Nigerian News Update,

Wakilinmu;

      👇🏻


Mahadi Tukur Almizan

DE YOUNG ACTIVIST

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post