Ⓜ--Daya daga cikin manyan yayan tsohon shugaban kasa, marigayi Alhaji Shehu Shagari, Aminu Shagari ya bayyana baci ransa da wasu abubuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, wanda a cewarsa hakan cutarwa ne ga mahaifinsu, kuma ya basu kunya matuka.
Aminu ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Punch, inda yace Buhari ya basu kunya matuka game da irin abubuwan da suka faru kafin mutuwar mahaifinsu da kuma bayan mutuwar tasa.
---Babban abin bakin cikin da Buhari yayi ma Shagari shine yadda ya kasance daya daga cikin wadanda suka yi masa juyin mulki a karshen watan Disambar shekarar 1983 jim kadan bayan ya sake cin zabe karo na biyu, inda Aminu ya bayyana hakan a matsayin cin amanar mahaifinsa daga wajen mutanen daya amincie mawa.
“Duk da cewa mahaifina ya yafe ma wadanda suka hambarar da gwamnatinsa, amma fa kamar duk wani mutum da ka sani, bai manta ba har rasuwarsa, kuma har ya rasu bai samu kulawar data dace da shi ba, musamman daga wadanda suka ci amanarsa ta hanyar juyin mulki duk da cewa basu kamashi da wata laifi ba.
“Haka zalika mun baiwa Buhari gudunmuwa wajen zama shugaban kasa, amma daya ci zabe bai sake waiwayar iyalanmu ba, ina ganin ya kamata ace ya kula damu sosai, musamman yadda ya yi ma mahaifinmu juyin mulki a baya duk cewa ya amince musu.
“Kuma a lokacin daya kawo mana ziyarar ta’aziyya bamu ji ya fadi maganganun da zasu kwantar mana da hankali ba, babu abinda yace bayan sanya hannu da yayi akan littafin masu ta’aziyya, na ji kunya sosai, domin na dauka a matsayinsa na Musulmi zai rubuta ‘Allah Ya jikansa…. Amma ba ko daya.” Inji shi.
___________________
Ma'asumiya Nigerian News Update,
Wakilinmu;
👇🏻
Mahadi Tukur Almizan
DE YOUNG ACTIVIST