Ⓜ---Munsamu Labarin sace wata karamar yarinya yar Islamiya mai suna Fatima Musa, da wasu yan bindiga marasa Imani suka yi garkuwa da ita a daidai lokacin da take kan hanyar komawa gida daga makarantar Islamiyya.
___Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Bashir Hashim ne ya sanar da haka, inda yayi nuni da cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 6 ga watan Janairu a garin Gusau, babban birnin jahar Zamfara.
Daliba Fatima ba ita bace farau ba da yan bindiga suka fara sacewa a jahar Zamfara, jahar da tayi kaurin suna wajen fuskantar ayyukan yan bindiga da masu garkuwa da mutane
__________________
Ma'asumiya Nigerian News Updates;
Wakilinmu;
👇🏻
Mahadi Tukur Almizan