ALBIRSHIR GAREKU YAN UWA,!!!


ALBISHIR GARE KU MAZAJE DAGA MATAN ALJANNAH !!!

* MA'ASUMIYA NIGERIAN NEWS UPDATES *

Uhmm, ku dage kawai da neman kusanci zuwa ga Allah ta hanyar bin dokokinsa, yunqurin tabbatar da addininsa, sada zumunci, kyautatawa, salloli da kuma azumummuka.

Kai ! Ku shirya tarar Bullet da Tankoki don kawar da zalunci da azzalumai a doron qasa, matan Aljannah na yabon kansu gare ku!

I know some one urged to hire from them.

Garajen me kake yi, garin da za ka tafi kana tambayar ya yake? Kai dai kayi addu'ah Allah ya kaika lafiya.

Abu Isah Altimidhi ya riwaito daga Ahmad Bn Muni'i, daga baban Mu'awiyata, daga Abdurrahman Bn Ishaq, daga Nu'uman Bn Sa'ad, daga Aliyu (R.A) yace, Manzon Allah (S.A.W.W) yace;

" LALLE A CIKIN ALJANNAH ZA A TARU DON (Matan) HURUL-EEN, ZA SU 'DAUKAKA WANI SAUTI WANDA HALITTU BA SU TABA JIN IRINSA BA". Yace,
" SUNA CEWA, " MUNE DAWWAMAMMU, BA ZA MU TSUFA BA. KUMA MUNE MASU BACCI DA ZA A TAYAR DAMU BA (sai dai mazajenmu), KUMA MUNE YARDADDU, BA ZA A TABA FUSHI DAMU BA. FARIN CIKI YA TABBATA GA WANDA YA KASANCE NAMU NE, MUMA NASA NE "!
(Tuhfatul-Ahwaz, J:1, Sh:156)
A riwayar Anas kuma yace, Manzon Allah (S.A.W.W) yace,

" LALLE HURUL-EEN ZASU RIQA YIN WANI YABO (gare su) A CIKIN ALJANNAH (suna cewa) MUNE 'YANTATTU MASU KYAUTATAWA, AN HALICCE MU NE DON KARRAMAWA GA MAZAJE "!
Yaa Allah, ka karrama mu da irin wadannan mata !!!

Daga wakilanmu na Bauchi Zone.
Tare da (Ado Isah Guda).
08137925034
Sa hannu Mas'udu Dan Masani Shinkafi 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post