BABU ADDU'AR DATAKE DA SHAMAKI A WURINA FACE ADDU'AR MACIYIN HARAM

-Imam Ali (AS) yace, “Mafi soyuwar aiki zuwa ga Allah a bayan kasa shine Addu’a.

-A wani hadisi Imam yace, Addu’a garkuwa ce ga mumini.”

-Manzon Allah (S) yace, “Shin in nuna maku wani makami wanda zai tseratar daku daga makiyanku, ya kuma bubbugar maku da arziki? Suka ce na’am, sai Manzon Allah yace kuyi addu’a dare da rana, domin makamin mumini shine Addu’a.”

- Imam Sadik (AS) yace, “Na horeka da yin Addu’a domin ita waraka ce ga dukkan matsaloli.”

KARANTA SAURAN LABARAN MUMU: ISAH ALMASIHU ZAI DAWO DOMIN YIN WASU AYYUKA BIYU..

-Imam Zainul-Abidin (AS) yace, “Addu’a tana tunkude bala’i wanda ya sauka da wanda bai sauka ba.”

-Imam Kazim (AS) yace, “Lalle Addu’a tana tunkude abin da
aka kaddara da kuma abinda ba a kaddara ba.”

-Yazo a hadisi wanda aka ruwaito daga Imam Sadik (AS) yace, ”Duk wanda yake so a amsa masa addu’arsa to ya tsarkake hanyar neman abincinsa.”

A wani hadisil-kudisi Allah Ta’ala ya ce, Babu addu’ar da take da shamaki a wajena face addu’ar maciyin haram.

Manzon Allah [S] yana cewa, “Ibada tare da cin haram tamkar gini ne kan yashi.”

-Akwai wani da yazo wajen Manzon Allah ya ce yana son Allah ya rika amsar addu’arsa, sai Manzon Allah ya ce masa, kada haramun ya shiga cikinka.

-Yazo a hadisi cewa wani lokaci mutum zai yi addu’a, Allah Ta’ala ya amsa masa, amma sakamakon aikata zunubi da yayi, sai ya zama masa shamaki daga samun biyan bukata.

-Yazo a cikin addu’ar Du’au Khumail “Ya Ubangiji ka gafarta min zunuban da suke tsare addu’a”
wato daga karbuwa,

a wani waje kuma aka ce “Ya Ubangiji ina rokon ka da izzarka kada mummunan aiki na ya shamakance addu’a ta”

-Muhammad Jiddah Nguru

08069306985

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Masha Allah Ƴan Uwa Allah ya saka muku da mafi girman Alherinsa

    ReplyDelete
Previous Post Next Post