Labari na
Cewar Abdurrazak Sani
Daga shafin Ma'asumiyya news updates.
A dai dai wannan lokacin da jawad ya kirani, bayan na zaiyana masa abin da yafaru, hankalin jawad ya yi mutukar tashi fiye da yadda me karatu ya ke tunani duk da cewar jawad lokuta da daman gaske ya na nunamin na boye akida ta tun da gidan mu nasan halin su, suna da zazzafar a kida ta kin Shi'a fiye da yadda mutum ya ke zato, ko ya ke tsammani, Amman da ya ke Allah (T) ya kaddara min sai na bar gidan mahaifina, sanadiyar zuwa taran ashura aminin Abban mu ya ganni, ya kuma shaidawa mahaifina.
Haka na taho kan hanya idanuna na zubar da hawaye babu kakkautawa, wani lokacin haka zan dan tsaya na yi kukana na koshi na godewa Allah, sa an nan na cigaba da jan akwatina me taya daya jakar tawa ta na bayana, wanda duk ya ganni yasan shakka babu babu lafiya. kirjina kuwa ya na cike da zaban tsagwaran bakin ciki maras musaltuwa. Haka na taho ban San ina zan nufaba, in banda jawad ya kirani ban San ina zan nufaba domin dangin mahaifiyata suna nesa domin ita yar jahar Adamawa ce. Amman duk da haka Maman mu ta yomin waya bayan fitowata daga gidan mahaifina bayan jawad ya kirani ta nunamin naje gidan kanin ta Wanda shima aiki ya kawo shi kano, Wanda shima Dan amutune a wannan kungiyar me kafirta musulmi, shiyasa tun farko ban nufi gidan sa ba, Wanda in abin na bayyana muku irin tsananin gaba da Shi'a da ya ke da shi wlh shakka babu za kusha mamaki Dari bisa Dari.
KARANTA SAURAN LABARAI:DAYA DAGA CIKIN HANYOYIN SAMUN KUDI A INTERNET
A haka na nunawa Maman mu zanje domin ita tashin hankalinta kadda na koma gidan jiya. Ina cikin wannan hali ina gefan titi ina tafiya ina Jan akwatina, idan na tsaya na yi kuka kana sa'annan na sa mashari na goge hawayen da ke fuskata, sannan na cigaba da tafiya.Bayan kimanin Rabin sa'a sai ga jawad ya karaso a cikin motar gidan su, ya na sanye da jallabiya fara, ga kuma (glass face) me dauke da nau'in fari, haka yazo ya yi parking sa'annan ya budemin kofa HANKALINA sa a tashe ka na na shiga muka muka tafi. A dai dai wannan lokacin motar mu ta daga kenany, sai ga babban aminin Abban mu ya taho da gudu a motar sa, (MA'ANA DAN IZALAN NAN DA YA GAMMU A LOKACIN DA MUKAJE ZAMAN A SHURA) ya nufo gidan mu, tana iya yiyuwa mahaifina shi ne ya kirashi domin yazo, haka muka hada ido da shi ya na cike da mamaki domin motar da muka je taran ashura jiya da ita, itace jawad ya dakko ko ya gane motar oho!.
Haka a wannan lokacin na ji kamar na je na cakumeshi domin shi ne ya yi sanadiyar barina gidan ubana, Wanda shakka babu shiryiwa ta Allah ce Wanda da adane bamuki mu haura gidan sa mu kashe shi ba har lahira, ko kuma duk yadda zamuyi mu bata masa suna wanda ko da mace ne zamubi duk yadda zamubi munga mun bata masa suna wanda wannan shi ya fi sauki. Amman sakamakon shirya ta Allah ce haka zalika SAYYID ZAKZAKY SHI NE SILA baya ga haka zamana Almajirin sayyid zakzaky da yawan sauraran karatuttukan sa yasa zuciyata ta sami imani fiye da yadda mutum ya ke zato, domin tabbas sayyid likitan zuciya ne na musamman, me shakka kuma ya gwada ma'ana ina nufin wadanda ba Shi'a ba, ya hanzarta ya saurari wasiyoyin Ameeral muminin (as).
Amman sakamakon tsoran Allah da kuma fauwalawa Allah (T) al amurana haka na barwa Allah naga cewar yaushe duniyar ta ke kuma kwanika nawane ta kare baki dayan ta?
Dandanan cikin wasu lokuta muka isa gidan su jawad da Isar mu, jawad yayi horn me gadi ya bude mana get cikin sauri. Gidan su jawad gidane Wanda shakka babu bazan iya musaltuwa ba baki dayan sa, Wanda kai daga ganin gidan su kasan lallai Abban su ya na DA kudi sosai, Amman duk da haka sun sami tarbiya fiye da yadda mutum ya ke zato.
Da shiga mu gidan jawad ya daka motar gidan su a wata kayatacciyar rumfa mai dauke da nau'in Kore da fari da wani irin nau'in kala Wanda bansan yasan iya fasaltawa ba, da Isar mu rumfar ga motocinan iri iri na alfarma da ta mahaifina su da ta Maman su DA sauran su. Haka muka fito daga cikin motar, jawad ya bude but ya dauko akwatina me taya ni kuma ina dauke da jakar gowo ya ce da ni, mu karasa Abdul haka muka nufi cikin gidan su, kuna tafiya A hankali abin abin banshawa'a.
Kafin mu karasa cikin gidan ban yi aune ba sai kawai na ji sautin wayata ma'ana ana kira,
KO KUNSAN WAKE KIRA NA KUWA!!!?
_sai abiyoni a kashi na Tara (9) don jin ya zata kaga....
Ku kasance da Shafin Ma'asumiya Nigeria News domin jin Cigaban labarin dama sauran Abubuwa.
RUBUTAWA: Daga Wakilinmu
Habib Rabiu Nasrallah
Editor: Mas'udu Dan Masani Shinkafi
Domin shawarwari kuna iyayi akasan Comments ko Ku Aiko mana Naku Labari ta Email dinmu: Mdanmasaniskff@gmail.com
Tags:
Labari Na