![]() |
Mas'udu Dan Masani Shinkafi ne lokacin daya kaiwa marwan Habibu Isa ziyara Garinsu |
Ilimin kiwon lafiya ilimi ne da ya kamata ace kowa ya san wani abu daga gare shi komai qanqantarsa. Saninsa zai taimakawa mutum akan kansa, kuma ya taimakawa wani.
Musamman a irin wannan lokaci da zalunci yayi yawa da kuma cututtuka, sakamakon fajircewa Allah da ake yi.
Manzon Allah (S.A.W.W) shine likitan likitoci, domin ya san abubuwan da matuqar mutum ya aikata su za su janyo masa cututtuka, haka kuma in ya nisanci wasu abubuwan lafiyarsa za ta qaru. Ya bayyana mana bai boye komai ba gare mu.
Sannan Sayyidah Fatimah (S.A) qwqrarriya ce wajen bada agajin gaggawa (First aid), kuma ta koyar da shi a aikace (practical). Ita ce ta fara bada agajin gaggawa (first aider), kuma akan mahaifinta (S.A.W.W) ta fara a yaqin UHUD.
Bari dai mu ji daga bakin ganau ba jiyau ba.
Bukhari yace, Qutaibata Bn Sa'id ya bamu labari, Ya'aqub ya bamu labari daga baban Haazeem cewa, ya ji ana tambayar Sahal Bn Sa'adin game da raunin (wounds) da aka yiwa Manzon Allah (S.A.W.W) ( a yaqin Uhud), sai yace,
" Amma wallahi ni na san wanda ya riqa wanke raunin da ke jikin Manzon Allah (S.A.W.W), da wanda ya riqa zuba ruwa, da kuma abinda aka yi masa magani da shi ."
Yace,
" Fadimatu (A.S) 'yar Manzon Allah (S.A.W.W) ta kasance ita ta ke wanke shi, Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A.S) yana zuba ruwa da Buta. To, a yayin da Fadimatu ta ga cewa babu abinda ruwan ke qarawa jinin face yawan zuba, sai ta yanki wani yanki daga Tabarmar Kaba ta qona ta, ta tattara ta (Tokar) ta tsayar jinin da shi. A lokacin shekarunsa (S.A.W.W) sunyi yawa, aka yiwa fuskarsa rauni (wound), kuma furfura ta yawaita a kansa ."
( Bukhari, Hadisi me lamba 4075 ).
Mata, ku dauki samfur daga Sayyidah (S.A) don amfanar da kanku da kuma al'umma.
Daga wakilanmu na Zone din Bauchi, Gombe da Adamawa.
Tare da (Ado Isah Guda).
Sa hannu Mas'udu Dan Masani Shinkafi
08137925034/08126385470