kayi Shere Domin wasu Su Amfana.
@Daga Shafin Ma'asumiya Nigeria News Updates
Alqawarin Allah ne na cewa zai gadar da wannan qasa tasa ga bayinsa salihai. Saboda haka duk zalunci, fasiqanci da fajircin fajirai zai zo qarshe ta hanyar dawowar ALMASIHU da bayyanar IMAM MAHDI (A.F).
AYYUKA BIYU NA ALMASIHU
__________________________
(1)- Allah madaukakin sarki na cewa;
" KUMA BABU WANI DAGA MUTANEN LITTAFI FACE SAI YAYI IMANI DA SHI KAFIN MUTUWARSA.... .."
(Nisa'i:159)
Idan mu kayi dubi da wannan ayar za muga cewa ai mutanen littafi ba gabadayansu ne su kayi imani da a matsayin bawan Allah kuma Manzonsa ne ba, domin suna cewa shi dan Allah ne. Saboda haka zai dawo don ya barranta da wannan furuci da suke yi na Allanta shi.
Muslim ya ruwaito cikin littafinsa game da bayyanar Dujal, a wani hadisi mai tsaho yana cewa;
KU KARANTA SAURAN LABARAI:KAMANCECENIYAR IMAM ALI (A.S) DA SAYYID ZAKZAKY (H).
" ISAH 'DAN MARYAMA ZAI SAUKO A WAJEN WATA HASUMIYA MAI HASKE TSAKANIN HARAMAI BIYU YANA MAI DORA TAFUKANSA AKAN FIFFIKEN MALA'IKU BIYU."
(2)- TAIMAKON IMAM MAHDI (A.F).
Cikin riwayar Abu Huraira yana cewa, Manzon Allah (S.A.W.W) yace;
" YA ZA KU KASANCE YAYIN DA 'DAN MARYAMA YA SAUKO A CIKINKU, KUMA LIMAMINKU (Mahdi) NA TARE DA KU?"
Cikin riwayar Bukhari da Muslim, daga Ibn Abbas (R.A) yace, na ji Manzon Allah (S.A.W.W) na cewa;
" WATA JAMA'A ('Yan Shi'ah) DAGA AL'UMMATA BA ZA SU GUSHE BA SUNA TSAYE QYAM HAR RANAR ALQIYAMA. ISAH 'DAN MARYAMA (A.S) DAGA CIKIN ANNABAWANMU ZAI SAUKO, SAI SHUGABANSU (Mahdi) YACE; " KAYI MANA SALLAH ". SAI YACE; " KU SAURARA! LALLE SASHENKU AKAN SASHE SHUWAGABANNI NE, KARRAMAWAR ALLAH CE GA WANNAN AL'UMMA ".
(Nurul-Absar, Sh:276-277)
Madalla da Almasihu mataimakin Imam Mahdi (A.F).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.