ANKULLA YARJEJENIYAR GUDANARDA HARKOKIN ZABEN 2019 CIKIN KWANCIYAR HANKALI DA ZAMAN LAFIYA
_________________________Ajiya talata ne 'yan takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyu daban-daban suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar gudanar da harkokin zaben 2019 cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya,
Duk da ba dukkan 'yan takarar kujerar shugaban kasa ne suka halarci taron saka hannu kan yarjejeniyar da aka yi a dakin taro na kasa da kasa ba,
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarta kuma ya saka hannu.
Wata cibiyar tabbatar da zaman lafiya ce ta shirya taron.
Abu 5 dake kunshe cikin yarjejeniyar zaman lafiya ta 'yan takarar shugaban kasa,
Ga kunshin abu 5 dake cikin yarjejeniyar da 'yan takarar suka sa hannu a kai;
1. Yin yakin zabe bisa doron abinda dan takara zai yi domin cigaban kasa a matakin tarayya, jiha, da karamar hukuma tare da gujewa yin amfani da addini da kabilanci yayin yakin neman zabe.
2. Gujewa yin kalaman da kan iya jawo barkewar rikici yayin zaben 2019 ko bayan zaben.
3. Yin biyayya ga yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattaba hannu a kai a gaban shugabannin addini, sarakuna, da manyan mutane masu mutunci a kasa.
4. Bawa hukumomin tsaro da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) goyon baya domin su samu sukunin yin aikinsu ba tare da nuna wariya ba.
5. 'Yan takara su fito fili su nesanta kansu daga kalaman tunzuri da magoya bayansu ko 'yan adawar su suka alakanta da su.
____________________________
Ma'asumiya Nigerian🇳🇬 News Update,
Wakilinmu;
👇🏽
Mahadi Tukur Almizan
Tags:
Labaran Duniya