Yau madai kamar jiya Almajiran Sheikh Zakzaky Sunyi Zanga zangar lumana agarin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya🇳🇬,
A cigaba da kiran asaki Jagoran Harka Islamiyya S Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah, wanda gwamnatin Nageriya ke cigaba da tsaresu tsawon shekaru uku kenan ba bisa wani laifi.
Bayan kisan kiyashin da Sojojin Nageriya yan ina da kisa sukayi akan almajiran Sheikh Zakzaky (H) din, da kashe masa Yayan da rusa masa muhallansa, bayan sunyi ruwan wuta akansu shida mai dakinsa, gobe Laraba 12/12/18 suke cika shekara uku a hannun hukamar Nageriya.
Sheikh Muhammad Abbari ya gabatar da jawabin rufe zanga-zangar ta yau Talata a garin Abuja, Sheikh Sidi Munir Sokkoto ya rufe da addu'a sai kuma gobe.
Ana gayyatar Al'umma zuwa gagarumar Muzaharar da zasu gudana cikin yan kwana kin nan, Laraba, Alhamis Juma'a, dan cikar shakara Uku da kama Sheikh Zakzaky (H) da mai dakinsa bayan kisan kiyanshi da akayi wa almajiransa.
_____________________
Ma'asumiya Nigerian🇳🇬 News Update;
Wakilinmu;
👇🏽
Mahadi Tukur Almizan
Tags:
Labaran Duniya