Ⓜ----yan ta’addan Boko Haram sun kwace garuruwa shida a jihar Borno
---- Garuruwan sune Baga, Doron-Baga, Kross Kawwa, Bunduran, Kekeno da kuma Kukawa
---- Wuraren sun kasance manyan cibiyoyi a karamar hukumar Kukawa da ke yankin arewacin Borno
------Rahotanni da ke zuwa mana sun yi ikirarin cewa yan ta’addan Boko Haram sun kwace garuruwan Baga, Doron-Baga, Kross Kawwa, Bunduran, Kekeno da kuma Kukawa a jihar Borno.
-----Daily Trust ta ruwaito cewa wata babbar majiya ta sojoji da siyasa ne suka bayyana hakan a Maiduguri a ranar Lahadi, 30 ga watan Disamba.
--An tattaro cewa dukkanin garuruwan guda shida sun kasance manyan cibiyoyi a karamar hukumar Kukawa da ke yankin arewacin Borno a yanzu haka babu dan Najeriya ko wata runduna a yankunan.
Yan ta’addan sun fara kai hari wani sansani na rundunar tsaro da ke Mil Hudu (wani yanki a wajen garin Baga) da misalin karfe 4pm sannan sojoji suka mayar da martani.
________________________
Ma'asumiya Nigerian News Update,
Wakilinmu;
👇🏻
Mahadi Tukur Almizan
DE YOUNG ACTIVIST
Tags:
Labaran Duniya