Ⓜ- Jami'an Hisbah jihar Kano sun sanar da kama wani matsahi mai shekaru 23 da laifin yiwa 'yan mata uku fyade
---Jam'ian Hisbah a jihar Kano sun sanar da cewar sun kama Suleiman Musa, matashi mai shekaru 23, bisa zarginsa da yiwa 'yan mata uku a gida daya fyade.
--Anshaidawa manema labarai cewar lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 27 ga watan Disamba, a unguwar Kurnar Asabe dake garin Kano.
----Musa ya zo unguwar ta Kurna ne a matsayin almajiri kafin daga bisani iyayen yaran su dauke shi yake masu aikin gida.
---Wani makobcin gidan da abin ya faru ya shaida wa majiyar mu cewar Musa ya yi amfani da yardar da iyayen yaran suka nuna masa wajen aikata laifin.
---Kazalika ya bayyana cewar an kama Musa ne yayin da yake cikin lalata da daya daga cikin yaran.
---A cewar makobcin, bayan an kama Musa ne aka gano cewar ya dade yana aikata haka ga yaran ta hanyar yi masu barazanar cewar zai yanka su idan suka fada wa iyayen su.
______________________
Ma'asumiya Nigerian News Update,
Wakilinmu;
👇🏻
Mahadi Tukur Almizan
DE YOUNG ACTIVIST
Tags:
Labaran Duniya